Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma'aikacin Zaɓe, Zai Iya Amsar Kyauta Daga Jam'iyyu ?

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum, Malam meye hukuncin kuɗin da jam'iyyu ke ba malaman zaɓe a lokacin zaɓe ? alhali su malaman zaɓen hukumar zaɓe za ta biya su kuɗin aikinsu? To malam kasan kowa da account number ɗin shi a wurinsu, jiya bayan na dawo gida sai aka min alert na kuɗin rumfar !

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, Wannan kuɗin da kuke amsa haramun ne kuma cin hanci ne, saboda an ba ka ne saboda kujerarka ta ma'aikacin zaɓe, inda a gidanku kake da ba su ba ka ba.

Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Abu-dawud ya rawaito "Duk wanda muka sanya shi wani aiki sannan muka yanka masa albashi akan aikin, to duk abin da ya karɓa bayan haka wuta🔥bal-bal ya ci".

 

Annabi S.A.W. ya fusata sosai kuma ya yi maganganu masu kaushi lokacin da ya aika IBNU-ALLUTBIYYA karbo zakka amma kuma sai aka ba shi kyauta ya karbe kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

 

Hadisan da suka gabata suna nuna cewa: haramun ne ma'aikacin da yake da albashi ko alawus ya amshi kyautar da aka yi masa saboda aikinsa, in har ya amsa kuma to ya ci wuta 🔥 rashawa.

 

Idan ma'akaicin zaɓe ya karɓi kyauta daga jam'iyyu, magudin zaɓe ba zai yi wahala ba, daga cikin salon magana a harshen Hausa "Duk Wanda ya mika hannu ba zai iya mike kafa ba" wannan yasa Musulunci ya haramta irin wannan Ihsanin.

 

Allah ne mafi sani.

 

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments