Ticker

6/recent/ticker-posts

Littafin Azumi [ 05 ] Me Ke Halatta Ga Mai Azumi?

• Haƙiƙa ALLAH TA'ALAH ya yi wa Musulmi sauƙi lokacin Azumi da daddare su sadu da iyalansu.

 ALLAH TA'ALAH ya ce:

An halatta gareku a daren Azumi ku kusanci matanku.

[Suratul Bakara: aya ta 187]

Ma'ana bayan an sha ruwa, ya halatta namiji ya yi kwanciyar aure da matarsa.

Barra’u ya ce: ya yin da ALLAH {S.W.T} ya wajabta Azumin Ramadan, sahabbai sun kasance ba sa saduwa da iyalansu da daddare, har sai da ALLAH ya saukar da wannan ayar.

 

• Babu laifi mai Azumi ya wayi gari da janaba a cikin watan Ramadan.

 Nana Aisha da Ummu-Salama (R.A) suka ce:

 

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance alfijir yana riskarsa yana mai janabar saduwa da iyalansa, sannan ya yi wanka kuma ya yi Azumi.

[Bukhari ne ya rawaito].

  Nana Aisha (R.A) ta ce:

Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana runguma ta lokacin da yake Azumi kuma nima ina Azumi.

[Abu Dawud].

Ma'ana yakan rungume matarsa da rana alhalin yana cikin azumi.

 Saboda haka dan mutum ya sumbaci matarsa koya rungume ta har ya fitar da maziyyi, to ba komai a gareshi, azuminsa yana nan.

 Idan kuma mutum ya rungumi matarsa ko ya sumbace ta, lokacin duk suna Azumi har ɗayansu ya zubar da maniyyi, to Azumin wanda ya zubar da maniyyin ya ɓaci kuma sai ya rama Azumi.

• Yin Ƙaho: Idan mutum yana Azumi sai ya sa aka yi masa ƙaho, shi ma ba komai a gareshi.

 Daga Ɗan Abbas (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi ƙaho a lokacin da yake Azumi.

[Bukhari ne ya rawaito].

• Sa Kwalli: Anas Ɗan Malik (R.A) ya kasance yana sa kwalli lokacin da yake Azumi.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments