Ticker

6/recent/ticker-posts

Kosan Nama Da Dankali

KAYAN HADI:-

  • NAMA
  • DANKALI
  • KWAI
  • ALBASA
  • ATTARUGU
  • GARIN BIREDI
  • CURRY
  • MAGGI
  • GISHIRI
  • TAFARNUWA.

KI SILALA NAMANKI DA ALBASA  DA TAFARNUWA DA MAGI DAIDAI DA GISHIRI KADAN, BAYAN KI SALILA KI DAKA YA DAKU SOSAI KI AJIYE A GEFE.

KI DAFA DANKALINKI KI MARMASA SHI, KI ZUBA NAMAN NAN A KAI,  KI JAJJAGA ATTARUGU DA ALBASA DAIDAI KI SAKA A KAI, KI SAKA MAGI DAIDAI, KI HADE SOSAI.

KI DINGA DAUKA KADAN-KADAN KI MULMULA SU, SAI KI SAKA A KWAI, KI CIRE KI SAKA A GARIN BIREDI KI SOYA, IDAN YA YI JA SAI KI KWASHE.

HAJIYA A GWADA YANA DA DADI SOSAI😋.

Post a Comment

0 Comments