Ticker

6/recent/ticker-posts

Juyin Waina

Matarsa ta ce: “Kwana biyu na rabu da ganin abokinka Abdul a gidan nan, Allah ya sa dai lafiya.”

Sai ya ce “Mun ɗan samu saɓani da shi kwana biyu, amma za mu shirya.”

Sai ta ce “Allah Sarki! Abdul mutumin kirki na san yanzu haka laifinka ne, ƙila kai ne ka ɓata mishi rai.”

Sai ya ce “ A'a ko kaɗan! Ce mishi na yi ina so in sayi mota da ƙuɗin da na samu a siyasar bana, shi kuma yake bani shawarar wai aure yakamata in ƙara tun da na samu dama,

Na nuna ƙin amincewa ta da shawararshi, shi kuma ya ji haushi ya ce kwata-kwata ba na son ɗaukar shawararshi, tun daga nan ko na kira a waya ba ya ɗauka.”

Sai ta ce “ Ƙyale ɗan banza!, Ni fa da ma kaf a cikin abokanka sam ban yarda da wannan mai ruwan munafukan ba.”🤣

Juyin Waina

Post a Comment

0 Comments