Ticker

6/recent/ticker-posts

In Kin Ɗauki Ciki A Bakin Aurenki

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Miji ne ya ce da matansa ta je asibiti tasaka abin ƙanyade iyali sai tace masa a,a itakan tana tsoro gaskiya sai mijin ya ce duk ranan da tasami juna biyu a bakin auranta Ana cikin haka sai tasamu shi ne na ce ya matsayin auran nata?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh Malamai sunada saɓani a kan wannan matsalar. Daga cikin Malamai akwai waɗanda suka ce matar ta saku saki uku. Wasu kuma suka ce A'a ta saku amma dai saki ɗaya ne. Wasu kuma suka ce ai batama saku ba tukunna harse an tambayi Mijin shin ɗaya ce idan tasamu ciki abakin aurenta mene yake nufi?? Idan ya ce saki yake nufi toh suka ce ta saku saki ɗaya. Inkuma ya ce A'a shi yafaɗane kawai dan ya tsoratata ta yi abun da yakeso amma baya nufin sake toh suka ce ba ta saku ba. Wannan shi ne ra'ayinda muka zaɓa insha Allahu. Ana iya duba Alwajiz Fi fiƙhis sunnah a babin saki.

Allah ya sa mu dace.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/ECƘsg2ycfS0FUI3fHfIdjƙ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments