Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Brush Da Makilin Da Rana Ayayin Da Mutum Yake Azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. Don Allah mene ne hukuncin sauran abincin da ya makale atsakanin hakoran mai azumi? Da kuma diddigar asuwaki wacce ta makale? Kuma mene ne hukuncin yin brush da makilin da rana ayayin da mutum yake azumi? Allah shi bada ikon amsawa, ya saka maka da mafificin alkhairin duniya da lahira. Ameen.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wabarakatuhu.

Sauran abincin dare wanda ya makale a hakorin mai azumi wajibi ne a furzar dashi kada a hadiye. Wanda kuma ya hadiyeshi da gangan to azuminsa ya karye sai ya rama. Hakanan diddigar aswaki itama wajibi ne a furzar.

Amma idan mutum yayi iyakar kokari wajen furzarwar, amma bai fita ba, Kuma ya wuce masa har cikin makogoro ba tare da saninsa ba, to wannan babu komai azuminsa yana nan.

 

Kasancewar Makilin yana da wani dandano mai Qamshi kuma alamar dandanon takan wuce har zuwa makogoro, to zai yi wahala mutum yayi brushi dashi ba tare da ya hadiyi dandanon ba.

Don haka Malamai suka ce ka iya yin brushinka amma ba tare da makilin din ba. Kamar yadda ya halatta kayi aswaki da kowanne irin itace marar dandado.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments