Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Jinkirta Ramukon Azumin Ramadan Har Wani Watan Azumin Ya Kewayo Bai Rama Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam ina da tambaya. ana bi na bashin azumi Sai ban samu na biya ba saboda rashin lapiya ina fama da laulayin ciki har wani azumin ya zo lokacin Kuma na haihu ban biya ba, to yanzu Kuma ina so in biya Sai dai banida abun da zan ciyar to zan iya biya koba ciyarwar?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Wanda ya jinkirta ramukon azumin Ramadhan har wani watan azumin ya kewayo, to sai ya azumci wannan din, sannan daga baya ya rama abin da ake binsa, bisa gwargwadon adadinsu.

Mazhabar Imam Hasanul Basariy da Imam Abu Haneefah sun tafi a kan cewa babu fidyah a kan mutum ko da bashi da wani uzurin da ya janyo masa jinkirin yin ramukon.

Amma Maluman Mazhabarmu ta Malikiyyah dasu da Imamush Shafi'iy da Imamu Is'haƙa 'dan Rahawaihi da Imamu Ahmad 'dan Hanbaliy duk sun yi fatawar cewar duk wanda ya yi sakaci wajen yin ramukon azumin Ramadhan har wani watan azumin ya kewayo, to ya azumci wannan na yanzun sannan daga baya ya rama wanda ake binsa.

Amma idan ya tashi ramawar sai ya hada da ciyarwa. Wato a kullum bayan ya yi azumin sai ya ciyar da miskini guda. (kamar adadin mudun Nabiy biyu na danyen abinci).

Amma wanda yake da wani halastaccen uzuri kamar jinya ko goyon ciki, (Wato kamar ke ke nan) to ba sai ya hada da ciyarwar ba, ramukon kawai zai yi.

Don Ƙarin bayani aduba littafin FIƘHUS SUNNAH na Shaikh Sayyid Sabiƙ, cikin shafin da ke magana a kan ƘADHA'U RAMADHAN.

WALLAHU A'ALAM.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

BASHIN AZUMIN BARA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene hukuncin macen da ta sha azumi amma har wannan watan na Azumi ya shiga ba ta biya ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Rama azumi ba dole ya zama a jere ba, saboda maganar Allaah (Sabhaanahu Wa Ta’aala) cewa

وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَر

Kuma wanda ya zama mara lafiya ko a cikin halin tafiya, to sai ya biya a cikin adadin waɗansu ranaku na daban. (Surah Al-Baqarah: 185).

Kuma kodayake rama azumman a cikin gaggawa shi ne ya fi, amma kuma ya halatta ya jinkirta shi har zuwa cikin watan Sha’aban. A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce

كَانَ يَكُونُ عَلَىَّ الصَّوْمُ مِنْ رَمَضَانَ ، فَمَا أَسْتَطِيعُ أَنْ أَقْضِىَ إِلاَّ فِى شَعْبَانَ .

Azumin watan Ramadan yakan kasance a kaina amma ba na iya ramawa har sai a cikin Sha’aban. (Sahih Al-Bukhaariy: 1950, Sahih Muslim: 1146).

Wannan ya nuna: Idan mutum ya yi sakaci wurin ramawa har watan azumin Ramadan na bana ya shiga, to ya yi laifin da sai ya tuba ga Allaah a kan haka. Kuma abin da ya ke wajibi a kansa shi ne: Ya yi wannan azumin na bana, sannan bayan sallah sai ya biya na bara.

To, ko akwai wata kaffara na ciyarwa a kansa sakamakon wannan jinkirin? Waɗansu malamai sun ce: E, wajibi ne a kansa duk ranar da ya rama azumin kuma ya ciyar da abinci ga matalauci.

Amma maganar da ta fi rinjaye a wurin malaman ita ce: Babu wannan ciyarwar a kansa. Domin ayar da ta gabata ramuko kawai ta ɗora masa, ba ta ambaci ciyarwa ba. Shi kansa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ma bai ɗora masa wata ciyarwa a bayan ramukon ba a cikin Sahihiyar Sunnarsa mai tsarki. (Tamaamul Minnah: 2/170-171).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments