Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shan Maganin Tsai Da Jinin Haila Saboda Kada A Sha Azumi

Amfani da maganin da yake hana haila ya halatta, idan ya zama bazai cutar da lafiyar jiki ba, amma idan zai cutar, to ya haramta saboda faɗin ALLAH TA'ALAH:

Kada ku jefa kawunanku a cikin halaka.

[suratu Albakarah aya ta 1952].

Sai dai duk da cewa hakan ya halatta da sharuɗan da suka

gabata, amma barinsa shi yafi, sai dai idan buƙatar hakan ta kama, saboda mutum ya zauna akan yadda yake yafi masa

kwanciyar hankali akan yayi abinda zai canza ɗabi’ar halittarsa.

Musamman ma wasu daga cikin ƙwayoyin na zamani suna rikitar da kwanakin haila, kamar yadda ya bayyana wasu matan da yawa suna fuskantar irin wannan matsalar, sai dai a kiyaye.

Don neman ƙarin bayani, duba :

Dima'uddabi'iyya

shafi na: 54.

ALLAH shi ne mafi sani.

HUKUNCIN MACE TA SHA MAGANI DOMIN TSAYAR DA JININ HAILA DON KAR TA SHA AZUMI

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam. Mene ne hukuncin mace ta sha magani domin tsayar da jinin haila don kar ta sha azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Sheikh Muhammad bin Saleh Al-Uthaimin (RahimahulLah) "Abinda nake gani a wannan batun shi ne cewa; mace kada tayi haka, sai dai ta tsaya akan abinda Allah Maɗaukakin Sarki ya hukunta ya kuma ƙaddara akan 'ya'yan Annabi Adam (mata), saboda wannan jinin haila da yake zuwa musu akowane wata Allah Maɗaukakin Sarki Yana da wata hikima wurin samar dashi, wanda wannan hikimar ta dace da yanayin mace, idan har ta tsayar da wannan dabi'a to wani abu zai iya faruwa wanda zai zama cutarwa ga jikin mace, kuma Annabi salati da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: "Babu cuta, babu cutarwa."

 Wannan Idan ma bamuyi la’akari da cutarwar da waɗannan kwayoyin suke haifarwa ga mahaifa ba kenan, kamar yadda likitoci suka ambata.

Dan haka abinda nake gani game da wannan mas'alar shi ne mata kada suyi amfani da waɗannan kwayoyin. Godiya ta tabbata ga Allah akan ƙaddararsa da hikimarsa. Idan hailarta yazo mata ta ajiya sallah da azumi, idan ya ɗauke ta sai ta fara sallah da azuminta, idan Ramadan ta ƙare ta rama abinda ake binta".

WALLAHU A’ALAM

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments