Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Bi Jam'in Sallar Jumu'a A Cikin Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ni ce na bi jam'in sallah juma'a ina cikin gida Sai kwana nan na ji wani wa'azi ba sallah ga wanda baibi jam'i ba ankusa shekara yanzu ya zan yi wajan gyara sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh yadda za ki yi shi ne za ki yi sallar azahar sabuwa yanzu amadadin waccan sallar jumu'an wacce bakiyiba kuma bakiyi azahar a makwafin ta ba, domin a shara'a duk mutumin da ya bi sallah ko da a cikin masallaci yake amma yaki shiga sahu toh kamar beyi wannan sallar ba ne, toh me kake tsammani ga wanda kuma shi dama bama a cikin masallacin yake ba kawai yana gidane kuma ya bi jam'in sallar toh wannan shi ma kamar beyi sallah ba ne. Idan aka duba cikin Littafin Akhda'ul Musallin na Siddeƙ Mishawi ya kawo hadisai daga Annabi inda ya yi sallah se daga baya ya hangi wani mutum ya yi sallar amma be shiga cikin sahuba, se Annabi ya umarceshi da cewa yatashi yasake sallah tun da be shiga cikin sahuba toh bashida sallah, toh ke me kike tunani tun da mutumin da yana cikin masallaci amma saboda kawai be shiga sahuba aka ce ya sake sallah toh ina kuma ga mutumin da ya bi sallar daga cikin gida??

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments