Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Karatun Alkur'ani Lokacin Khuduba Jumu'ah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Shin ya halasta ana Khudubar juma'a mutum yana karatun Ƙur'ani?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Toh shi Musulinci addini ne me tsari wanda yake ajiye kowanne abu a kan muhallinsa. Dan hakanan ita Khudubar Jumu'a wata ibada ce ta musamman wadda kawai abun da aka ce kai me sauraren huduba ka yi shi ne ka yi shiru, kawai shirun ake so ka yi ba'aso kace komai dan haka yin karatun Alƙur'ani a sadda ake huduba toh shi ma lagawu ne wanda ze iya sabbabawa mutum ya yi asarar ladan sallar jumu'ar tashi gaba daya. Dan haka ba a yin komai in ana huduba ko wa'azi ba'ayi kuma ba a gyara ɓarna matukar ba bisa laruraba. Aduba Taisirul Allam na Ali Bassam za a ga karin bayani.

Allah ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments