𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam da fatan kana lafiya, Allah ya sa haka. Malam tambaya ne dani kamar haka: Wato malam nine na kasance a dalilin abokan banza suka rinjayeni har takai an yi lalata dani (wato LUWAƊI) amma yanzu na tuba na yi istingafari to amma akwai abin da yake damu na adubura, Sai na rika jin kamar motsi, to shi ne na ce malam don Allah ka taimake ni kamar yadda Allah ya temakeka ka fadi min maganin da zan yi amfani da shi ko shawarwari. Allah ya kara basira.
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikas salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika bawan Allah ka aikata babban laifi daga cikin
mafiya sharrin kaba'irorin da Allah ya haramta.
LUWAƊI laifi ne wanda ko dabbobi
ba sa yin sa. Don haka Allah ya haramtashi kuma ya tsine wa masu yin sa. a
cikin suratul Anbiya (alaihimus salam) Allah ya ambaci mutanen Annabi Luut
(alaihis salam) cewa "HAKIKA SU MUTANEN BANZA NE FASIƘAI"
Sannan a cikin suratu Huud da suratul Hijri da
suratush Shu'ara Allah ya fa'di irin yadda ya halakar da su da kuma mummunar
azabar da ya fara gana musu tun daga nan duniya. Allah ya yi bayanin cewa
"MUNYI MUSU RUWAN DUWATSUN WUTA AKANSU".
Abdullahi 'dan Abbas (rta) ya ce Mala'ika Jibreelu ne ya ciccibi birnin nasu ya dagashi sama sosai sannan ya kifar da su sannan Allah ya yi musu ruwan duwatsu daga karkashin wutar jahannama. Duk wannan azabar an yi musu ita ne saboda girman laifin da suka aikata ɗin ne, wato LUWAƊI. Kuma kai ma nasihar da zan yi maka a nan ita ce: yin istighfari kaɗai ba zai zama mafita gareka ba, har sai ka yi sahihiyar tuba irin wacce Allah ya yarda da ita. Bayan ka yi nadama azuciyarka, wajibi ne ka ɗauki niyyar nisantar wannan aikin har abada a cikin rayuwarka, sannan ka kaurace ma waɗannan abokan naka, da su da duk mutanen da ke yin lalatar daku, sannan ka nisanci duk wani dalilin da zai iya kaika zuwa ga komawa cikin lifin.
Sannan game da motsi ko kaikayin da kake ji a duburarka, ina shawartarka ka gaggauta zuwa asibiti ka samu manyan likitoci su duba lafiyarka, su auna jininka domin gano abin da ke damunka da kuma tabbatar da cewa baka dauke da wata mummunar chutar.
WALLAHU A'ALAM.
Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DTrJJCF04ƘpACEtA7hyu4R
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.