Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kara Wa Amarya Yawan Kwanaki, Saboda Honey Moon

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Tambaya meye hukuncin mutumin da yana da mata sai ya yi amarya sai ya yi mata visa suka tafi wata kasa wata ɗaya a matsayin honey moon, to meye hukuncin daya matar, ya zalunce ta ke nan?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikum assalam. To ɗan'uwa Anas (R.A) ya rawaito cewa: "Yana daga cikin sunnah In mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya yi mata kwana bakwai, in kuma bazawara ce kwana uku" kamar yadda ya zo a Sunanu Attirmizi a hadisi mai lamba ta: 1139, wannan sai ya nuna kari a kan haka ya saɓa wa sunnah.

Amma Idan Uwar gida ta bada izni ya halatta a yi kari a kan haka, tun da ya halatta mace ta sarayar da hakkinta na kwana, kamar yadda Saudatu ta bawa Nana A'isha kwananta, lokacin da girma ya zo mata, ta ga Annabi bai damu da ita ba sosai, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4914,

Wannan sai ya nuna halaccin sarayar da hakkin kwana, da yiwuwar yi wa amarya kari idan uwar gida ta yarda.

Allah mafi sani.

✍️ DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments