Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Fitsari Da Kashin Dabbar Da Ake Cin Namanta

Fitsari da kashin dabbar da ake cin namanta mai tsarki ne, saboda abin da ya tabbata daga Anas Ɗan Malik (R.A) ya ce:

 Wasu mutane sun zo Madinah, sai suka yi ta rashin lafiya,

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya aikasu wajen Raƙuman sadaka don su riƙa shan fitsarinsu da nononsu.

[Bukhari ne ya rawaito shi].

Duk wata dabba da aka halatta cin namanta kashinta da fitsrinta ba najasa ba ne, ko da kuwa ya zuba ajikin tufafin mutum ne.

 Da a ce mutum zai yi alwala ya tafi masallaci sai akuya ko rago su yi masa fitsari to wannan fitsarin ba najasa ba ne, ko da baisa ruwa agurin ba, zai iya yin sallarsa a haka,

 Sai dai kawai zai iya wankewa ne saboda tsaftace jiki daga ƙarnin fitsarin amma bawai dan fitsari ko kashinsu najasa ba ne.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments