Mu San Hukunce-Hukuncen Fiƙhu [ 19 ] – Hukuncin Cin Mushe

    HUKUNCE-HUKUNCEN MUSHE

    Mushe shi ne abin da ya mutu da kansa batare da yanka na shari'a ba, ko kuma abin da aka yanko daga jikin dabba mai rai kafin a yanka ta.

    MUSHE YA KASU KASHI-KASHI

    • Mushen kifi da Fara.

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    An halatta mana mushe biyu, da jini biyu, mushe biyu su ne, mushen kifi da

    mushen fara, Jini biyu kuma su ne, hanta da saifa.

    [Ahmad ne ya rawaito shi].

    Saboda haka su waɗannan abubuwa sun halatta aci mushensu, ba a shar'anta sai an yanka su ba kafin aci namansu,

    Sai dai a sarrafasu ta hanyar dafawa ko suya ko gashi, kuma kashinsu da fitsarinsu ba najasa ba ne.

    • Mushen abin da jini baya gudana a jikinsa.

    Kamar Ƙuda:

     

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Idan ƙuda ya faɗa a cikin kwanon ɗayanku, to ya dulmiya shi gaba ɗayansa, sannan ya cire shi ya jefar, saboda a fiffi-kensa ɗaya akwai waraka, a ɗayan kuma akwai cuta.

    [Bukhari ne ya rawaito shi].

    Shi ƙuda a fukafikinsa ɗaya akwai cuta shi ya sa idan ya faɗa cikin abu mai ruwa-ruwa sai ya dulmiya ɓarin jikinsa ɗaya, kuma wannan ɓarin shike ɗauke da cuta.

     

     Hakan ya sa nusantar da idan ya faɗa cikin abun sha to a dulmiyashi dukkansu sannan sai a cire shi, ko da ya saka cuta a cikin abin shan, to ana dulmiyashi cutar za ta fita.

    • Naman Alade.

     ALLAH TA'ALAH ya ce:

    Kace, ban samu abin da yake cinsa haramun ba ne cikin abin da aka yi min wahayin sa, sai dai idan mushe ne ko jinin da yake kwarara ko naman alade, haƙiƙa shi ƙazanta ne.

    [An'am ayata:145].

    Shi naman Alade gaba ɗayansa haramun ne, ko da mutum zai mutu da yunwa ko da a cikin daji ne bai halatta ya ci naman alade ba.

    • Kare:

    Kare gaba ɗayansa najasa ne, najasar yawunsa kuma mai tsanani ce, saboda Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Tsarkin kwanon ɗayanku idan kare ya yi lallage a cikinsa, shi ne ya wanke shi sau bakwai, ya sa ƙasa a wanki na farko.

    [Bukhari da Muslim].

    Abin da ake kira lallage shi ne, kare ya sanya harshensa ya jujjuya shi a cikin kwano, ko ya sha abin da yake ciki, ko bai sha ba.

    Shima kare cin namansa haramun ne, yawunsa najasa ce mai tsanani, haka kuma ajiyeshi a gida dan ado haramun ne, sai dai ya halatta a ajiyeshi da nufin gadi ko farauta.

    ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.