Ticker

6/recent/ticker-posts

Ango Ya Rasu Kafin Amarya Ta Tare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. An ɗaura auren wasu yau ba a ɗauko amarya ba sai gobe, amma Allah ya yi wa angon rasuwa. tambayata a nan wai shin za ta yi takaba? Kuma tana da gadonshi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

To dan’uwa idan miji ya mutu bayan an ɗaura aure kafin ya tare da amariyarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a ba ta gadonta cikakke, kamar yadda Annabi (SAW) ya yi hukunci da hakan ga Barwa’u ‘yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments