Ticker

6/recent/ticker-posts

Malam ni budurwa ce kuma gobe za a ɗaura mini aure zan zama amarya, wace shawara za a ba ni da kuma wasiyya?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu alaikum wa rahmatul laah. Mallam Ni budurwa ce kuma gobe za a ɗaura mini aure zan zama amarya, wace shawara za a ba ni da kuma wasiyya?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. 

Shawarar da za a baki ba ta da yawa kuma ba ta da amfani har fa sai idan za ki aiki da ita.

Da farko dai, ki yi haƙuri, domin aure ibadah ne, kuma ba wata ibadah da ke yiwuwa sai da haƙuri. Ki zamo mai tsoron Allah da taķawa, hakan bai samuwa sai da zuwa makaranta. Don haka ki maida hankali wajen neman ilmi.

Ki zama mai cikakkiyar biyayya ga Allah da Manzonsa kafin ga mijin ki. Haka ki so mijin ki, amma ki fifita son Allah da Manzonsa a kan son sa. Ki sani wannan zama na aure da duk abin da zai haifar ibadah ne.

 Ki zamo mai biyayya ga mijin ki har ki fifita biyayyar ki a kan ta iyayen ki, biyayyar Allah da ta Manzo Allah kaɗai ke fin ta shi a matsayin sa na mijin ki. Ki girmama iyaye, yan'uwa da aminan sa.

 

Ki zamo mai yawaita addu'ar alkhairi gare shi a ko da yaushe. Ki zamo mai wadatuwa da duk abin da ya iya baki, sannan ki gode masa. Ki kula da tsabta da canja girki mai daɗi a kai a kai. Ki ji, ki yi kamar baki ji ba, ki gani kiyi kamar baki gani ba. Ki guji almubazzaranci da tozarta masa dukiya ko abinci in ya kawo, ki zamo mai tattali. Ki zamo mai raha a labarin ki da shi.

A wannan farko zaman na ku, ki ƙoƙarin gane abin da yake so, ko ki tambaye shi, da irin abin da baya so don ki guji yi masa su da ganganci. 

Kar ki dinga bashi labarin kawayen ki. Ki guji kai labarin ku na sharri, a wurin yan'uwa ko iyayen ki. Kina da damar farun albarkacin bakin ki, amma da kin hararo zai koma musu, toh ki kame bakin ki. Haka a lokacin saɓani da ɓacin rai, ki koyi bashi haƙuri. Ki zamo mai taimakon mijin ki da karfin ki da dukiyar ki. Ki zamo mai tausayin mijin ki. Mijinki ya zamo abokin shawarar ki ba wanin sa ba.

Daga ƙarshe kar ki dauko salon zaman wasu ma'aurata ki kawo gidan ki, sai na alkhairi. Wannan kaɗan ne daga cikin abin da za a baki na Shawara. 

Wallahu ta'ala a'lam.

 Amsawa:

 Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments