Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Ke Karya Azumi (Littafin Azumi 06)

• Ridda, wato fita daga Musulunci.

• Ci ko sha da gangan ba tare da uzuri ba.

• Haila ko Nifasi, sai a ƙirga kwanakin da aka sha a rama su bayan Ramadan.

• Jima'imutum ko dabba ko ma da mene ne.

• Fitar maniyyi dan sha'awa ko da jima'i ko babu.

• Kakaro Amai da gangan.

• Ciwon Hauka.

Da sauransu.

Idan namiji da mace suka sadu da rana a cikin watan Azumi to, azuminsu ya ɓaci, sai su rama kuma suyi kaffara, idan kuma mijin ne ya tilasta ta, to shi zaiyi azumin kaffara, ita kuma zata rama azumi ɗaya ne.

 Abu Huraira (R.A) ya ce:

Wata rana Manzon ALLAH {s.a.w} yana zaune sai wan mutum yazo yace, ya Rasulullahi, na halaka, sai Annabi ya ce dashi, mai ya halaka ka?

Sai ya ce: Na sadu da matata a cikin watan Azumi da rana,

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce dashi, zaka sami abinda zaka ’ƴanta bawa?

Sai ya ce: A’a,

Sai ya ce: Zaka iya yin Azumi watanni biyu a jere?

Sai ya ce: A'a.

Sai ya ce: Shin zaka sami abinda zaka ciyar da miskinai sittin?

Sai ya ce: A’a,

Sai mutumin ya zauna a wajen Annabi {s.a.w} har aka kawo wa Annabi buhun dabino.

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce dashi, ɗauki kayi sadaka dashi,

 Sai ya ce: Ai duk cikin Madina babu wanda ya fi ni buƙata.

Sai Manzon ALLAH {s.a.w} ya yi dariya har sai da haƙoransa suka bayyana.

Sannan ya ce: Ɗauki kaje ka ciyar da iyalanka.

 [Jama’a da yawa ne suka rawaito]

Wannan hadisi yana mana nuni da hukuncin wanda ya karya azuminsa da ganganci,

Idan mutum ya afkawa matarsa da rana ana azumi, har ya yi nasara akanta ya biya buƙatarsa, to zai rama Azumi 60.

Ita kuma matarsa zata rama Azumi ɗaya tak, saboda ba ita ta neme shi ba, shi ne ya neme ta, da ita ta neme shi, to ita ma sai ta yi Azumi 60.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments