Akwai kayan haɗin da ake buƙata yayin haɗa kuɗin gyaɗa. Yana da kyau a lura da cewa, waɗansu daga cikinsu ba dole ba ne (kamar madara ko lemon tsami). Amma samun su zai ƙara wa abin armashi matuƙa.
i. Gyaɗa
ii. Kayan ƙamshi
iii. Lemon tsami
iv. Madara
v. Ruwa
vi. Shinkafa
vii. Suga
Da farko, akan gyara gyaɗa sannan a jiƙa ta. A gefe guda kuma, za a wanke shinkafa kaɗan (amma za a yi la’akari da adadin gyaɗar da yawan kunun da ake son yi) ita ma sai a jiƙa ta. Bayan sun jiƙa, za a haɗa su a kai markaɗe. Za a sanya kayan ƙamshi kafin a kai niƙa. Da zarar an dawo da shi daga markaɗen, sai a yi amfani da matata domin tacewa. Bayan an tace, sai batun damawa da ruwan zafi. Ba dole ne a tanadi gasara ba a wannan nau’i na kunu. Idan an kammala dama kunun, ana iya sanya masa lemon tsami da madara. Suga kuwa da ma, “farilla ne tusar mai bacci.”
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.