Ticker

6/recent/ticker-posts

Ranakun Da Aka Hana Azumin Nafila (Littafin Azumi 06)

 • Ranakun Idi guda biyu, wato ranar ƙaramar sallah da babbar sallah.

• Haka kuma kwanaki ukun da ke gaban ranar babbar sallah (Ayyamut tashrik) sai da uzuri.

• Keɓantar ranar Juma'a kawai, saidai ka haɗa ta gabanta ko ta bayanta.

• Keɓantar ranar Asabar kawai, sai dai ka hada gabanta ko ta bayanta.

• Haka kuma ranar shakku, kamar ana zaton gobe Ramadan zai kama ko kuwa.

• Haka nan yin Azumi ba hutawa kullum.

• Haka nan matar da mijinta yake nan a gari sai da izininsa.

• Haka nan jeranta Azumi ba tare sahur ko buɗa baki ba, a yi kwanaki ana haka.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments