Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Jagora: Yara ku tashi,
Za ni Wamakko,
Yara: Don mu ishe,
Barade garkasa.
Jagora: Yara ku tashi,
Za ni Wamakko,
Yara: Don mu ishe,
Barade garkasa.
Jagora: Kai ka halin Barade
Jaɓɓi,
Ka yi halin ruwa mai sondale,
Ka yi halin Barade Aliyu.
Jagora: Sarakunnan ga da ni
lisafa,
Martaba su tana hannunka,
Yara: Kai ka faɗi a yarda ko dole.
Jagora: Sarakunnan ga da ni
lisafa,
Martaba su tana hannunka,
Yara: Kai ka faɗi a yarda ko dole.
Jagora: Ai ga wane ya yi ɓamɓarama,
Yai magana ga ta wahalshe shi,
Yara: Ga gidansu ya yi mai
nisa,
Yana kware wurin gadi.
Jagora: Ai ga wane ya yi ɓamɓarama,
Yai magana ga ta wahalshe shi,
Yara: Ga gidansu ya yi mai
nisa,
Yana kware wurin gadi.
Jagora: Yau kai ka faɗi a yarda Wamakko,
Duw wani ƙulle-ƙulle an bar shi.
Jagora: Yau kai ka faɗa a yarda Wamakko,
Yara: Duw wani ƙulle-ƙulle a bar sa.
Jagora: A Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Baraden Wamakko,
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Baraden Wamakko.
Jagora: Ina mawaƙa,
Iana maroƙa.
Jagora: Ina mawaƙa,
Ina maroƙa,
Wani mai waƙa da arashi,
Ko mai roƙo a soke-soke,
Kun ga gidan Barade Jaɓɓi,
Sai ga gidan Barade
Aliyu,
Sai ga gidan ruwa mai
sandale,
Sai ga gidan Barade
Gainaku,
Kun ga abin ga duk gida ɗai ne,
Yara: To na hore ku ‘yan
uwana,
Duk wani soke-soke an daina.
Jagora: Ina mawaƙa,
Ina maroƙa?
Jagora: Ina mawaƙa?
Ina maroƙa?
Wani mai waƙa da arashi,
Ko mai roƙo da zage-zage,
Kun ga gidan Barade Jaɓɓi,
Sa da gidan ruwa mai sandale,
Sa da gidan Barade Aliyu,
Sai da gidan Barade Gainaku,
Kun ga abin ga duk gida dai na,
Yara: To na hore ku ‘yan
uwana,
Duk wani soke-soke an daina.
Jagora: Alhaji Ɗangaladima,
Ɗan sarki mai aikin
sarki,
Alƙawalin da ya yi ya
ida,
Yara: Mota wadda ya hwaɗa ya bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Alhaji Ɗangaladima,
Ɗan sarki mai aikin
sarki,
Alƙawalin da ya yi ya
ida,
Yara: Mota wadda ya hwaɗa ya bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Sakataren Gwadabawa
Garba,
Abubakar Ɗan yari Sadauki,
Alƙawalin da ya yi ya
ida,
Yara: Mota wadda ya faɗa ya bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Sakataren Gwadabawa
Garba,
Abubakar Ɗan yari Sadauki,
Alƙawalin da ya yi ya
ida,
Yara: Mota wadda ya faɗa ya bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Ɗanyarin Wamakko
Garba,
Yara: Mota wadda ya yi
bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Ɗanyarin Wamakko
Garba,
Yara: Mota wadda ya yi
bai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Bello Haliru
sadauki,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: A ni ai Bello Haliru Giwa ku gai sai,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: A Ɗanhaliru Bello na
Giwa,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: A haji Muntari haji
mai gona,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A haji Muntari haji
mai gona,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A haji Bello Isa na
gode,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: A haji Bello Isa na
gode,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Ga wani ya yi biɗa an kasai,
Ya ga sarauta tai masa nisa,
Ya sai homa da mamari nai,
Boyi Kabawa na ga nai,
Yara: Ya koma yini cikin
tafki.
Jagora: Ya koma boyin
Kabawa,
Yara: Ya koma yini cikin
tafki.
Jagora: Can ni gaa nai boyin
Kabawa,
Yara: Ya koma yini cikin
tafki.
Jagora: Ga wani ya yi biɗa an kasai,
Ya ga sarauta taimasa nisa,
Ya sai homa da mamari nai,
Boyin Kabawa ni same shi,
Ya koma yini cikin tafki.
Jagora: A Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Baraden Wamakko.
Yara: A Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Baraden Wamakko.
Jagora: A ubandawaki Giɗaɗo ku gai sai,
Yara: Daraja Barade ya ba
mu.
Jagora: A ubandawaki Giɗaɗo ku gai sai,
Yara: Daraja Barade ya ba
mu.
Jagora: A Ubandawaki na
gode,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Wani ɗan sarki ya lalace,
Domin wane ba ya alheri.
Yara: Sai in ya ga macce
ta wulga.
Jagora: Wani ɗan sarki ya lalace,
Domin wane ba ya alheri.
Yara: Sai in ya ga macce
ta wulga.
Jagora: Wani Ɗansarki ya lalace,
Shi dai wane ba ya alheri
Yara: Sai in ya ga macce
ta wulga
Jagora: A Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko,
Yara: A Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko,
Jagora: Yau Wamakko,
Yara: Don mu ishe Barade
garkarsa.
Jagora: Mu je Wamakko yara
in huta,
Yara: Do mu ishe Barade
garkassa.
Jagora: Birnin Wamakko ya yi
daidai,
Kai ka hwaɗi a yarda don dole.
Jagora: Birnin Wamakko ya yi
daidai,
Kai ka hwaɗi a yarda don dole.
Jagora: A birnin Wamakko ta
yi daɗi,
Yara: Kai ka hwaɗi a yarda ko dole.
Jagora: A birnin Wamakko ta
yi daidai,
Yara: Kai ka hwaɗi a yarda ko dole.
Jagora: Audu sifika na
gwamna Aliyu,
Audu sifika na gode ma,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A Audu sifika na
gode ma,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Haji Audu sifika,
Audu na gwamna,
Yara: Don daraja Barade ya
a mu.
Jagora: Ina sifika na jaha
ya yi,
Audu Balarabe salamu.
Jagora: Ina sifika na jaha
ya yi,
Audu Balarabe salamu.
Jagora: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Jagora: Ai ga wane ya yi ɓamɓarama,
Yay maganar da ta wahalshe shi,
Yara: Ga gidansu ya yi mai
nisa,
Yana kware wurin gadi.
Jagora: Ar ga wane ya yi ɓamɓarama,
Yay maganar da ta wahalshe shi,
Yara: Ga gidansu ya yi mai
nisa,
Yana kware wurin gadi.
Jagora: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kwan da shiri Barade Wamakko,
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Amshi: Duka ‘yan
Wamakko na yi ma murna,
Ga ka da gwabna ka yi sarauta,
Naka naɗi yana cikin sa’a.
Amshi: Duka ‘yan
Wamakko na ta murna,
‘Yan Wamakko na yi ma murna,
Ga ka da gwabna ka yi sarauta.
Jagora: Naka naɗi yana cikin sa’a.
Amshi: Salihu,
Yara: Naka naɗi yana cikin sa’a.
Jagora: A gwa ka da gwamna
ka zama sarki,
Yara: Naka naɗi yana cikin sa’a.
Jagora: In ga ka da gwamna
ka zama sarki,
Yara: Naka naɗi yana cikin sa’a.
Jagora: Haji Umar sarkin roƙo,
Ummaru Ɗan’ama
na gode,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Ga riguna manya ga
kuɗi,
Ummaru Ɗan’ama
Madawaki,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Eee ga riguna ga
manya kuɗi,
Umaru Ɗan’ama
Madawaki,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Amshi: Zama da masoyi
yana da daɗi,
Ina Babangida tashi hwaci,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A ina Babangida
tashin gwaci,
Yara: Don daraja barade ya
ba mu.
Jagora: Umm, Salihu ba a jan
karan yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Jagora: Na gode Aminu dodon
iya,
Don daraja Barade ya ba mu.
Jagora: Rai ya daɗe Aminu Dodo Iya,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A cif akawonta na
gode,
Aminu Dodo Iya ka kyauta,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Ni Bello Haliru
birnin Giwa,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Ya ban mota saboda
gwamna,
Jagora: Ya ba ni mota sabo
da gwamna.
Haliru na gode ma,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A ni Bello Haliru
Giwa,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: Na je Wamakko Ɗanba’u,
Na ishe wane ransa ya ɓaci,
Ko abin bai yi mai daɗi ba,
Na ishe wane ranshi ya ɓaci,
Shin ko abin bai yi masa daɗi ba?
Na ishe wane ransa ya ɓaci.
Jagora: Imm Salihu ba a jan
ka ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Jagora: Ɗan sarki in ba ya
biyayya,
Kulbadaɗe yana zama ƙutal.
Jagora: A Ɗansarki in ba
biyayya,
Yara: Kul baɗaɗe yana zama ƙutal.
Jagora: A ‘yan sarki ku bi
sarki daidai na,
Ɗan sarki in ba ya
biyayya,
Yara: Kul badaɗe yana zama ƙutal.
Jagora: ‘Yan sarki ku bi
sarki daidai na,
Ɗan sarki in ba ya
biyayya,
Yara: Kul badaɗe yana zama ƙutal.
Jagora: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Yara: Salihu ba a jan ka
ran yaƙi,
Kar ka sake Barade Wamakko.
Jagora: A sakatare birnin
Wamakko,
Abubakar S.Gari Illela,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A sakatare birnin
Wamakko,
Abubakar S.Gari Illela,
Yara: Don daraja Barade ya
ba mu.
Jagora: A uban Magaji S. Gari Garba,
Don daraja magatakarda ya ba mu.
Jagora: Baba Magaji S. Gari Garba,
Yara: Don daraja
Magatakarda ya ba mu.
Jagora: A Ɗanmalikin Illela kai ɗa na gaishe ka,
Mai gidan hogan,
Yara: Don daraja Barade ya ba mu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.