Ticker

6/recent/ticker-posts

"Garkuwa Ga Sahabbai" - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.


Alu Sarkin Yamma garkuwa ga sahabbai,

Fari ahalissunna ne na Allah wutiri.

 

Da sunan Allah nake yabon sayyadina,

Ta’ala, mulkinsa shi ya mamaye ko’ina,

Huwal ƙadiru muƙtadir Jazah bul hasana,

Tabaraka Allah Maɗaukaki mai ji na,

            Ka yaye mana wahhala a dukkan lamari.

 

Aminci tsiranka ya Ilahis samadi,

Ka ƙara shi ga Ɗaha wanda shi ne sanadi,

Ga dukkan bayinka gunka shi ne mahadi,

Wasila ya Rabbana daɗo ba adadi,

            Maƙamal Mamudu sai imamul Mamadi.

 

Da dukkan matansa Sidi Abdul Fɗima,

Kamar A’ishatu da Zainab Ummul Salma,

Da Sayyada Khadijatu da Maimunatu ita ma,

Da dukkan matansa Ummahatul ulama,

            Da ‘ya’yansa dukansu masu hali na gari.

 

Da dukkan assahabu masu tsantsar ilimi,

Kamar Sidi Abubakar da Umar jarumi,

Da Usman Affan da Ali ƙofar ilimi,

Dukan kulafa’ur rashidina taskar ilimi,

            Da dukkanin wanda an ka wa alƙarari.

 

Da dukkan auliya’u masu hali na gari,

Kamar Shehu Tijjani da shi da Abdul Ƙadiri,

Da Shehu Ibrahimu mai yabo gun Bashari,

Da Shehu Usmanu bini Fodiyo na wutiri,

Ala zummatu Mustafa abin alfahari.

 

Salamu alaikum ya’yan uwa tare da ni,

Da wanda suke nesa hankalinku ku ba ni,

Nufina ku taho mu ƙari junanmu sani,

Mu laiƙa hadisai mu dubi Alƙurani,

            A kan ƙaunar ashabu za mui nazari.

 

Farillane kan dukan Musulmi na gari,

Bauta wa Rabbu babu kawo uzuri,

Da ɗa’a ga gwani sannan ya zyo gun Bashari,

Son Allah da Manzo da ‘yan gidan Aɗɗahiri,

            Da karatun Ƙurani ya kauce wa haɗari.

 

Sannan ya iso ga waɗanda sunka yi yo dace,

Da sun kai ladabi ga Ɗaha sunka amincie,

Allah ya yarda da su da yarda tasa ce,

Da yai musu albishiri da aljannarsa ce,

            Da yac ce sun sami tsira ran ashari.

 

Su ne fa sahabbai a gun imamum Bashari,

Da ƙaunar manzo ta sa su kay yo katari,

Allah ya shaide su kan ɗabi’a ta gari,

Da Allah ya yabe su ɗahirai ne na gari,

            Duk mai ƙyamar kowanensu ya shiga haɗari.

 

Dalilina na gani cikin Ƙurani ne,

Inda Allahu yake yabon sahabban Ɗaha ne,

Da yac ce sun tsira ran ƙiyama haka ne,

Da yai musu tanadi gida na aljannatu ne,

            A dan haka ƙauna gare su bautan wuturi.

 

Allah ya ce ga Mustafa majiya na arashi,

Da waɗanda su kai imani da ad tare da shi,

Sun yi jihadi dukiyoyinsu ba ƙyashi,

Kuma sun yi da rayukansu don ƙaunar shi,

            Suna da alkairi masu yawa inji wutiri.

 

Ya ce yai musu tanadi a ranar tsayuwa,

Yac ce sun sami tsira ne da yawa,

Da yab ba su gidan Aljanna domin taƙawa,

Da yac ce shi ne rabo mafi girma kuwa,

            Duk mai ƙaunar su babu shi ba garari.

 

Son Allah shi ne son manzo ku yo nazari,

Son sahabban Ɗaha so ga manzo Bashari,

Idan ka ƙi sahabu ka warware alƙawari,

Da kaɗ ɗauka tun kana ciki ka yo ƙudiri,

            Idan ka tuba Ilahu zai ma uzuri.

 

Dukan hujja babu ita ban ganta ba,

Suka ga sahabu ba hali mai kyau ba,

Da auren mutu’a fa ba koyin Annabi ba,

Da ƙazafin da su kai ba za ni furta muku ba,

            Zan ce yai muni su tuba domin wuturi.

 

Dalilin da na ce Aliyu sarkin Yamma,

Ya zam garkuwar sahabu ba ƙarya ne nai ba,

Domin bai yarda a soki ko wanne ba,

Ya ce da su kowat tuba Ilahu zai yafe mai,

            Idan sun ƙi ba za shi ƙyale ko ɗai a gari.

 

Jama’ar Sokoto da duk su kay yo gangami,

Sun ka zaɓi mujahidi ƙwararre jarumi,

Sun so mai gaskiya sahihin malami,

Da ya hana ɓarna ya sa magabta nai gumi,

            Allahu ya ba mu shi sahihi na gari.

 

(Sokoto yake faɗa, shi ya sa na rubuta haka).

 

Alu ahlis-sunna ne fa ba ƙarba ba,

Dalilina zan faɗa ba zan noƙe ba,

Da yaz zam bautar Ilahu yas sa a gaba,

Ya daidaita sahu ya yo fa in kun duba,

            Da komai zai yo fa zai yi domin Wuturi.

 

Alu bai wasa da bautar Ilahu gwani,

Ma’abocin salla ne ga shi mai imani,

Da yas samu rabo da ba shi yin gunguni,

Sannan ko da yaushe yana karanta Kur’ani,

            Ba ya raina aikin lada akwai shi da ƙoƙari.

 

Yana so domin Gwani ya ƙi domin Gwani,

Yana yarda don Gwani fa bai gunguni,

Yana umurni da aikin alkairi ne masani,

Yana hani ga dukkanin mai muni an sani,

            Kyawun hali nai ya zaga ƙauye da gari.

 

Mai halin ƙwarai da ba shi yin alfahari,

Da ke girmama baƙi da mutanen gari,

Yana girmama maƙwabta Alu mai nazari,

Mai ƙaunar jamaa da munka samu na gari,

            Ba ya ƙwange ko kaɗan abin alfahari.

 

Alu bai kibiri fa ko fushi don garari,

Mai halin kyauta gwamnanmu mai alkairi,

Da ba ya ƙyamar konannenmu mai haƙuri,

Abin ƙaunar jamaa ta ƙauye da gari,

            Ƙwararre mai juriya ga kowa jari.

 

Alu rabbil mukazzibina ne ba mai ja,

Da munka yi mubayi’a fa mun san hujja,

Da yaz zam garkuwar sahabu ba ja-in-ja,

Yardadden shugabanmu babbar hujja,

            Allah yai baiwa gare shi mai kyan sadari.

 

Amintacce ba ka cin amana haka ne,

Amintacce mai yawaita kyauta mani,

Mai alkunya da laddabi da kamun kai ne,

Mai tsantseni mai halin girma ga kowane ne,

            Muna nan bayanka ba ka saɓa alƙawari.

 

Abin so mai taimako ga kowa ne ma,

Da ke kyautata rayuwarmu ne mai himma,

Da ilmi da Rabbi yay da kowa ya nema,

Mutuntacce ne Aliyu Sarkin Yamma,

            A gai da na Allah na Mustaɓa na Bashari.

 

Ba ya wasa gun fitar da zakka ne shi,

Ya sauke faralinsa ya yi aikin hajji shi,

Ma’abuci na umara da ba ya ƙyashi,

Alu ya sam albarkanmagabatanshi,

            Sannan ya riƙi yan uwansa mui yo nazari.

 

Mijin Hajiya Arziki da Murjanatu ne,

Baban Mahadi da Fodiyo da Lamiɗo fa ne,

Mahaifin Isa Alu da bai cara ne,

Abin alfahari na Sarkin Musulmi ne,

Sa’ad Abuabakar da ke da hali na gari.

 

Tamat an nan zan dakata a wannan shiri,

Baban Halima Kaduna ne fa marar fikiiri,

Da sam ban da sani barai ya sa ai marari,

Shaiƙi yas sa ni baituka nai nazari,

            Na yo don ƙauna ga gwamna ne kai nazari.

Post a Comment

0 Comments