Ticker

6/recent/ticker-posts

"Mun Yi Mubayi’a" - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa. 

Mun yi mubayi’a gun Alu Sarkin Yamma,

Don mun san ba za mui ɓatan ɓakatantan ba.

 

Bismillahi ya Rabbana mai shiryarwa,

Arrahmani mai ni’ima ma ishin yalwa,

Shi ne wanda baiwarsa ba ta ƙarewa,

Sai dai in ko ɗan Adam bai gode ba.

 

Buwayi Ubangijina ka tsarkaki niyyata,

Ya masanin cikin zuciya da buƙatata,

Ka biya mana buƙata Tabaraka mai kyauta,

            Don baiwarka Allahu ba zai ƙare ba.

 

Na roƙe ka Allahu ninka salatinka,

Gun Manzonmu Ɗaha fiyayyen bayinka,

Shi ka zaɓa ka aiko da Alƙuraninka,

            Alaye da ashabihi ban ware ba.

 

Tun da a fari nas sanya Mahaliccin kowa,

Na yi salati ga Musɗafa mai buɗewa,

Duk ni’ima ta Allahu wacce ka kullewa,

Cikamakin Annabawa da manzannin Rabba.

 

Kafin in wuce baitukan da na yo ɗoɗar,

Zan yi tawussuli don biɗar yardar Jabbar,

Gaffir sayyi ati Ilahu wala tu’akir,

 Magafirati ya Rabbana ba don ni ba.

 

Ya Ƙahharu don Musɗafa baban Fati,

Ka tsare zuciyata ga aikin sayyi’ati,

Kamar mai shan maɗaci a ce masa zo ga tea,

            Ka san ai ba zai yi gardama ya ƙi shayin ba.

 

Na san zuciyata tana da yawan datti,

Kai kumka Rahimu ne mai yafe sayyi’ati,

Tun da na kama ƙafa da Ɗaha abal Fati,

            Na san Rabbi ba za ka sa in yi kunya ba.

 

Yanzun zan wuce cikin baitoci zalla,

Gun wannan da kowa ka ce mai madalla,

Mai ƙaunar Maaiki da bautar Jallalla,

Sarkin Yamma mai taurayi ba sauna ba.

 

Sakkwato ta yi haske da ba a taɓa samu ba,

Dondacewa da wanga alhairi babba,

Sarkin aikimai taurayi ba tababa,

Ma’abucin kyauta da bai san rowa ba.

 

Ribar demokoraɗiya da ba musani ba,

Mulkin baya ba a bar mu mun miƙe ƙafa ba,

Yanzuko Alu ne da bai san handama ba,

            Koko wawura ba hali nai tambaɗa ba.

 

Jama’ar Sakkwato tunda muka haɗe kanmu,

Muka zaɓo Aliyu Sarkin Yamma a hammu,

Mu zamo tsintsiya maɗauri ɗaya babu gammu,

            Kowa za ya murmure ba tababa ba.

 

Kowa ya sani Alu mai kyan tsari ne,

Mahaƙurci mawadaci kuma mai ilmi ne,

Mai cika alƙawar ne da bai ƙyashi ga wane,

            Mai aiki don Rabbu ba don ya burge ba.

 

Mun yi mubayi’a ga Alu ba mu noƙe ba,

Don la shakka shi ne madubin dubawa,

Tun da Ilahu yab ba shi bam mu butulce ba,

            Don mu sam ba zai turbuɗa mu a rami ba.

 

Mulki dai na Allahu ne in kun gane,

Wanda ya so yake baiwa ko ba sisi ne,

Wayo ko zaƙewa da izza duk ƙarya ne,

            Ba sa jure ƙaddarar Jalla gwani Rabba.

 

Ba ja tun da ma Alu muka samo lale,

Ya yi nassaara don hakan mun yi lale,

Gwamnatin kowa da kowa ba ƙulle-ƙulle,

            Dama ta samu babu ƙyashi ba zamba.

 

Ahalan wa sahalan ya abin ƙauna babba,

Ma’abocin mutunci da ba ya yin zamba,

Da ba shi riƙo balle a ce ma yai gaba,

            Mai haƙuri mai tausayi ba sauna ba.

 

Tunda wuri riƙon amana Alu ya gada,

Halaye na girma da alkairi da yarda,

Yas sa munka dage a zaɓe babu ganda,

            Ƙwammu da kwarkwata munka zaɓo ɗan babba.

 

Sarkin Yamma ƙaunarka ba ma dainawa,

Sakkwato mun miƙa wuya ga Alu ɗan baiwa,

Yau da gobe har jibi ba ma canzawa,

            Ba ma yarfe ko tsangwama ko kankamba.

 

Sakkwato tin da mun zaɓi namu sahihi ne,

Mu yi haƙuri mu ba shi dama ya yi aiki ne,

Kadda mu bar magauta su ci mu da yaƙi ne,

            Domin na ga ‘yan adawa ba su mazaye ba.

 

‘Yan adawa ku daina yin hauma-hauma,

Bakin alƙalam ya riga ya bushe ma,

Tun da Ilahu yab ba Alu Sarkin Yamma,

            Shi ne alkairi ƙwarai ba wancan ba.

 

Da ma tun fil azal adawa taki ce,

Ita kan sanyo a ci gaba a haƙiƙa ne,

Tun da wuri ake wa Alu har yai dace,

Bai yo martani ko kaɗan ga adawar ba.

 

Damo sarkin haƙuri Alu baban Mahdi,

Baban Fodiyo ne barunmu ruwan daɗi,

Babban malami gwamna mai ɗumbin sodi,

Ma’abocin farin jini ba ƙarya ne ba,

            Murucin kan dutsi abin ƙauna babba.

 

Baba Alu haƙiƙa ƙwarai mun yarje ma,

Tun da mu kai ruwan ƙuriu ranar fama,

Nasara ka yi sai du’ai’I fa muke yi ma,

            Don mun san da kai da wancan ba ɗai ne ba.

 

Sakkwato tun da mun gane da an yo ɓarna,

Mu ko mun ka yi dace Alu yaz zam gwamna,

Da hawa tai munka samu ‘yanci ba ɓarna,

            Duk mun murmure ƙorafi ba mu koma ba.

 

Ba a taɓa yin gwamna kama tai Sarkin Yamma,

Mai sauraron jama’a ba ya yin ƙyama,

Gida nai kulli yaumin da tarin al’umma,

            Tun da ya hau bai bar lamarinmu da yunwa ba,

 

Na yi kira ga Sakkwatawanmu ku sakunne,

Domin ‘yan a ɓata suna nan mun gane,

Tun da anka kaffa gwamnatin sun rikke ne,

            Sun yi shirin wulaƙanta dun mabiyan baba.

 

Suk ka ce du wanda yab bi baba Alu take,

Ma ci baƙar wuya ko a bi mu a yanyanke,

Sunayen masoya Alu duka sun ɗauke,

            Suka ce dole su ne da nasara ba mu ba.

Post a Comment

0 Comments