Ticker

6/recent/ticker-posts

Dokin Karfe - Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

Dokin Ƙarfe - Waƙar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU)

Mun tantance mun amince,

Dokin ƙarfe ya fi keke,

Mai tauran talakawa sannu,

Baba Alu babba ɗan babba.

 

Wanda ya ƙagi guna da goji,

Shi ne yai zakaru da kaji,

Yai lukuki shi yai maji,

Yai ƙarami kuma yai yi babba.

 

Rabbi maƙagin fili da ɓoye,

Duka shi yai ‘yan tagwaye,

Allah don matsayin iyaye,

Ka yarda na tsara batu a karɓa.

 

Tsira harda aminci ɗin nan,

Ƙaro gu nai annabin nan,

Ali sahabu da shenan nan,

Jikokin gun ɗan Suwaiba.

 

Ba don badon ba  sai in ce,

Zan dai yo magana a taƙaice,

Zance ne ba ƙauce-kauce,

Ba fa batun ƙarya nake ba.

 

Ya jama’a mu taho dukanmu,

Wanda muke ta biɗa ya samu,

Aliyu kairi ne gare mu,

Gwarzon ƙwarai ba zai gaza ba.

 

Mulkin baba abin yabawa,

Har abada kairi bai gushewa,

Alkairi ya nashe kowa,

Kun ga ko sam ba za mu bari ba.

 

Aliyu ga mu gabanka damƙam,

Kay yi mai-mai kai za mu zaɓa,

Don ba ka zam mai wariya ba,

Balle ka yi ƙyashi da zamba.

 

Ya angon su Arziki sannu,

Kyakkyawa mai kyan idanu,

Sarkin yamma mai ihisanu,

Na Hajiya Murja bai yi faɗa ba.

 

Baban Yasira da Mahadi ne ma,

Baban Fodiyo da Isah ne ma,

Baban Bello da Jamilu Ɗan girma,

Mahaifin Lamoɗo sannu baba.

 

Sarkin Yamma na sarkin Musulmi,

Sa’adu Abubakar Imami,

Mai baiwar tausai muhimmi,

Ƙauna gun ku ba za mu bari ba.

 

Tamat nan ni zan yi birki,

Na gode Allahu sarki,

Da ya ban iko nay yi aiki,Nai waƙa ga baba.

 

Wanda ya tsaro baituka ne,

Baban Halima marar sani ne,

Mai koyo ne ni ku gane,

Don baitoci ban iya ba.

Post a Comment

0 Comments