Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.
Bambancin
Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 43)
Baban Manar Alƙasim
Daya daga
cikin matsalolin maza a shimfida, wanda shi ke gadar da rashin jin dadin
uwargida, shi ne saurin kawowar da maigida yake yi, tabbas mace ba kamar namiji
take ba, ita ko ta kawo tana iya yin haƙuri da
maigida, amma shi in ya riga ta to ba wani abin kirki da zai iya tabukawa,
wannan ya sa, halittar mu a al'adance ita ce mace ta riga maigidanta isa gari,
in kuma ya riga ta zuwa sai ya jira ta su sauka tare, in kuwa ba zai iya jurewa
ba to ya tabbatar yana da rauni, mafita kawai sai ya fara kai ta kafin ya iso,
a nan ne aikin dan-tsaka zai taso, kamar dai yadda muka yi bayani a baya.
Kowani maigida
ya ji tsoron Allah, ya gane cewa cutarwa a addinin muslunci haramun ne, kuma
irin waÉ—annan abubuwan
da yawa in ba neman gafarar wanda aka cuta aka yi ba Allah bai yafe wa mutum,
masamman in da a ce ita macen ce ta ƙi amince wa
maigidan ya biya buƙatarsa ba za a kwashe da lafiya
ba, kowa sai ya ji tsakaninsu, sabo da haka alhakin biyan buƙatar uwargida
yana kan maigidanta, in ba shi da ƙarfin da zai
kai ta ƙololuwa sabo da saurin kawowa da yake yi, to ya bi
daya hanyar, wato motsa dan-tsaka, da tsotson 'yar-tuluwa, ba shakka nan da nan
za su ingiza ta har inda take buƙata, kawai dai
maigida ya tabbatar ya wanke hannunsa da sabulu sabo da tsoron infection.
Abu Ghait ya
ce " Wannan matsala ta saurin-isa ta yi yawa a tsakanin samari a yau"
[Masamman mazauna birane, yadda za ka taras da saurayi bai dauki kwankwadar
sukari a bakin komai ba, duk abin da zai sha sai ya antaya sukari, ga shan
lemon kwalba, wani kullum sai ya sha kwalba daya a rana, akwai wanda in ya daga
wannan ƙaton kwalbar sai ya zazzage ta, wata ƙila kuma ya ma
ƙara da wani abin, in ya tashi diban gasasshen jan
nama ya ci da yawa, shi wannan bai da illa ta kai tsaye.
Amma abin da
yake faruwa shi ne, ya dibgi nama mai gamsasshen kitse, ya sha ruwa mai sanyi
ko lemon kwalba mai bala'in sukari, ya je ƙarƙashin fanka ko
ma AC ya sami wuri ya kwanta, wata ƙila kuma da
tashinsa ya sami ruwan sanyi ya watsa, ya za a yi namiji ba zai zama rago a
shimfida ba? Abin da ya sa matasan karkara suke riƙe da ƙarfinsu koda
yaushe shi ne, ba su da kudin shan waÉ—annan lemon kwalban koda yaushe, amma suna cin
'ya'yan bishiyoyi da ganyayyaki, su kuma wannan suna ƙona maiƙo ne da
maganin ƙananan cututtuka, ba su da kudin cin gamsasshen maiƙo koda yaushe,
in ma suna ci din dai za ka gan su a gonakinsu suna aiki, su sha zafin rana
sannan ga isasshen motsa jiki.
Matar da ta
auri tsoho a karkara, matashi a maráya ba zai iya gamsar da ita ba, masamman
wanda bai motsa jiki sai aikin ƙwaƙwalwa mai
dama, daga nan za mu fahimci cewa raunin da matasammu suke fama da shi a yau su
ne suke jawowa kansu, ta wurin dibar gamsasshen kitse, sukari na wuce hankali
da rashin motsa jiki, mata sukan dan sami sauƙin wannan don
kashi sittin da wani abu cikin dari suna motsa jininsu ta wurin ayyukan cikin
gida ne, share nan, wanke can, kawar da wannan jawo wancan, wace ba ta motsa
jikinta ta fi samun sanyin jiki sama da mai aikace-aikace a cikin gida, zuwa
aikin gwamnati ba shi ne maganin matsalar ba, akwai bambanci a tsakanin stress
da exercise, wato gajiya ko motsa jini].
Abu Ghait yake
cewa "Akan sami kashi 10 cikin 100 na mata ba sa samun isa ƙololuwa a
lokacin saduwa sabo da wasu 'yan matsaloli" ya ce "Amma tabbas in za
a kula da aikin dan-tsaka nan da nan za a kai su" [Matsalar da muke samu a
yau za ta iya kasuwa zuwa kashi biyu, ta farko ita ce: Jikin mace kamar sauran
abin hawa ne masu hayaƙi, ba yadda za
a yi su fara tafiya sai an tayar da su, shi ya sa ko a fiƙihun saduwa
aka ce Annabi ya ce a samar da dan saƙo, wato magana
mai daga sha'awa a tsakanin ma'aurata, kenan auka wa mace ba tare da motsa
sha'awarta ba yana iya aukar ma ta da sanyin shimfida, a ƙarshe ba abin da
za ta iya yi.
Irin wannan fiƙihun duk wani
namiji yana da buƙatarsa, in ya kasance gurza ba
za ta iya tunkuda uwargida zuwa ƙololuwa ba, to
sai a koma tsotson 'yar tuluwa, da shafar dan tsaka don ƙarisar da ita,
amma masana kamar yadda na karanta, sun yi harsashen cewa waÉ—an da ba su da
aure bai kamata ba samsam su gwada waÉ—annan hanyoyi don kai kansu inda Allah bai kaisu ba,
suka ce hakan yana da illoli da dama ta bangaren lafiya, rayuwa, da
zamantakewa, sai kuma addini da dabi'u na ƙwarai sun ƙi haka gaba
daya.
WaÉ—an da ba miji
da mata ba in suka sami kansu a irin wannan yanayi, to ba shakka wani ƙoƙari ne na:-
1) Koyon zina,
a lokacin da ƙarfi ya kai mutum ya sami lada ga shi yana neman
daukar zunubi.
2) A maimakon
a zakke wa dan adam an dawo saduwa da hannu.
3) Yakan kawo
tursasa mabubbugar mani ta yi aikin da ya fi ƙarfinta a dan
lokaci kadan, tana iya gazawa in aka nace.
4) Rashin
samun cikakken sha'awar da zai tatso mani din, wanda in hakan ya yi yawa to
wasu gabobin za su iya raunata ciki har da zuciya.
5) Ba dabi'a
ta ƙwarai ba ce namiji ya riƙa ƙoƙarin ya fitar
da mani da kansa kamar yadda jaki yake yi, bayan Allah SW ya sauwaƙe masa hanya
mai dadi, kuma mai lafiya ga tarin lada, kamar yadda hadisi ya tabbatar da
haka.
6) Dimantuwa a
kai yakan karya ƙudurar namiji ko mace a wurin
saduwa, ta yadda ba za su iya kaiwa wannan ƙololuwar ba
sai ta wannan hanyar, idan mutum ya nace yin haka tabbas jijiyoyinsa suna iya
gaza yin aiki da kansu a lokacin saduwa.
7) Wasu
malaman sun fassara yin hakan da cewa zina ne kai tsaye.
Anan Zan
Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na
Gaba
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.