Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 42)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 42)

Baban Manar Alƙasim

Mata da miji

Rauni irin na shimfida abu ne da aka sani yana samun maza da mata, sai dai likitoci da masanan fannin sun bayyana cewa ya fi samuwa a tsakanin maza din, a wani littafi da na karanta na sami cewa matan da suke da rauni a shimfida ba su wuce 5% ba, in aka hada da maza sai ka ga kamar ba a samun rauni gaba daya a mata, to amma in za mu fassara abin kamar yadda Mal. Yusuf Abu Ghait ya ce ne sai mu ga cewa adadin ya wuce yadda suke magana nesa ba kusa ba, masamman ma in muka zo maganar ma'anar rauni din.

Abu Ghait ya ce " Rauni irin na shimfida, galibi, yana nufin samuwar ƙarancin adadin maimai ne na saduwa, wanda da ana su zai nuna cewa shi kammalallen namiji ne, ko kuma gajartar tsawon lokacin da mutum zai iya kwashewa kafin ya waiwayi mace, wani ma yakan sami watanni bai kula mace ba, [ Alhali in aka sami lafiyayyen namiji a karkara zai iya zagaya shimfidarsa sau uku ma a dare daya, wani har da ƙari, don haka a nan kawai an sami abu biyu, kodai gajiyawa a yayin saduwa, ko kwashe tsawon lokaci ba a waiwayi mace ba].

"Wani abu kuma zai bayyana wanda ake ganin shi ne babban matsala, wato samun guntuwar mazakuta, ko sanyi irin na mace ko na namiji, waɗan da suke sanya mutum ya gaza biyan buƙatar shimfidarsa kamar yadda ya dace, koma ta kasance bai da sha'awar kusantar iyalin sai dai ya yi kawai tsoron magana ko tashin hankali, [ Yadda za ka san akwai matsaloli, duk malamin da ya tabo wannan batun, za ka sami mata da dama sun saurara ko ma su riƙa yi masa wasu 'yan tambayoyi, irin waɗannan tambayoyin ne za su nuna cewa akwai matsalar a zagaye da jama'a, babban abin takaici mazan kuma ba sa son a yi maganar samsam, kuma suna ƙyamatar ta, kuma babu wata hanya ta yin maganin matsalar, ba a ma shirya ma ta ba].

Koda yake mata ma sukan sami irin waɗannan matsalolin, amma in aka lura da bayanan BBC na baya can sai a taras mazan ne ba sa son su bi musu ta hanyar da za su iya biyan buƙatunsu, a daidai lokacin da in shi namijin bai sami biyar buƙata ba ba sauran zaman lafiya, da sannu in mace ta ci gaba da samun ƙarancin kulawa dangane da biyan buƙatunta na shimfida sai ta fara yi masa tutsu, masamman in ta taba yin aure a wani wuri kuma ta san yadda abin yake a can.

Wasu mazan da dama sukan ƙi auren bazawara da wannan hujjar, domin su sami yarinya wace suke da tabbacin ba ta san komai ba, su riƙa biyan buƙatunsu suna barinta a cikin baƙin ciki, wata ko ta san ga yadda abin yake ba za ta iya kai ƙararsa ko da kuwa wurin uwayenta ne ba, don a ganinta abin kunya ne a ce tana ta da jijiyar wuya a kan shimfida.

Wata sai dai ta yi ta kuka ita kadai, ko ta sami ƙawarta ta riƙa gaya ma ta abin da yake damunta, wata ba ma ba wanda yake sanin abin da ke faruwa sai dai kullum a riƙa samunta cikin rikici ita da maigidan, duk wanda ya yi ƙoƙarin raba su kuma sai dai a ƙarshe ya rabu da su ya kama gabansa don ba zai ci nasarar gane wa ke da matsala a tsakaninsu ba, irin wannan matsalar tana da wuyar magani, don babu cutar da ake maganinta bayan ba a tantance ta ba.

A zahiri da mace za ta riƙa gudun namiji na tsawon mako guda kawai, in dai shi yana da buƙatar ta nan da nan za a ji tsakaninsu, wannan ya sa nake ganin neman magani a wurin namiji abu ne da yake wajibi, za mu dan tattaro wasu 'yan magunguna da muke ganin ya zama wajibi mu kula da su, sai dai yana da kyau mutum ya san cewa don yana haihuwa ba shi ne yake nufin lafiyarsa lau a shimfida ba, haka kuma don ba ya haihuwa ba shi ne yake sa a gane cewa bai da lafiya ba.

Abu Ghait ya lissafo wasu dalilai da yake ganin su ne suke janyo raunin mutum a shimfida ta bangaren halitta, ciki har da damuwa da tashin hankali, cutar sukari, ƙarancin ƙwayoyin sinadarin Andurojin a cikin jini, samun matsala a wasu ayyukan hanta, yawan shan barasa; giya, ƙwayoyi da sauransu, matsalolin jijiyoyi, kamar kumburinsu da rauninsu, ko yin wani aiki a bangaren da ya shafi maraina ko mabubbugan mani, shi ya sa ake yawan tsoratar da maza ga sanya matsattsun kaya, bare kuma mata waɗan da masana iliminsu suke yawan tsoratar da su game da haka.

Ta bangare zuciya ma ana iya samun abubuwan da za su raunana namiji, masamman wanda yake cikin damuwa amma duk da haka yake ƙoƙarin saduwa da iyali, ko kuma ita din ce take da matsala kuma take ƙoƙarin saduwa da maigida tare da tsammanin samun biyar buƙata, koda yake hanyoyin samun raunin suna da yawa, amma akwai wanda yake ganin har da tabbataccen tsoro na ganin ba za a sami haihuwa ba, wani kuma ya ce: Yawan tashin-tashina ne da rashin fahimta a tsakanin ma'aurata yake kawo rashin natsuwar da rauni kan sami damar kurdadowa, har ya yi musu illa.

Post a Comment

0 Comments