Wannan littafin yana ƙunshe ne da wasu keɓaɓɓun kalmomin fannu da kuma maganganun azanci da hikima, waɗanda suka yi tasiri a rayuwa da falsafa cikin al'ummar Sinawa. An zaɓo sannan aka fassara irin waɗannan kalamai guda ɗari biyu (200) daga cikin ɗari uku (300), da manyan masana fiye da guda ɗari (100) daga ƙasar Sin da Turai suka yi bayani a kansu. Wannan aiki wata sabuwar hanya ce ta bunƙasa ilimi dangane da falsafar al'ummar Sinawa da tarihi da kuma aikin fassara. Wato aikin fassara kamar kullum, yana wakiltar sabuwar hanya ce ta isar da saƙonni ga al'ummu daban-daban. Domin sauƙin fahimta, kowace kalma ko maganar azanci tana tafe da ƙarin bayani dangane da ma'ana da kuma yadda ake amfani da ita a tarihin al'ummar Sinawa. Ga al'ummu na ƙasashen duniya kuwa, waɗannan muhimman batutuwa za su share fagen fahimtar falsafar rayuwar al'ummar Sinawa ne a gida da waje.
Farashi: #2,500 kacal.
Tuntuɓi: Prof. Salisu Ahmad Yakasai
Lambar Waya: +2348035073537
Imel: syakasai2013@gmail.com
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.