Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 34)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 34)

Baban Manar Alƙasim

 3) Yana da matuƙar amfani kuma a sami daidaituwar manufa a tsakanin manema ko ma'aurata, ta yadda in wannan yana son abu za ka iske wancan ma yana matuƙar buƙatarsa, kwanaki wani abokina yake ba ni labarin matsalar da wasu ma'aurata suka sami kansu a ciki, ya ce sun dan girma amma shi maigidan mai son sakewa ne da walawa, yana da dan abin hannunsa kuma yana fantamawa yadda yake buƙata, to amma ita matar tana ganin wannan yaranta ce, tunda shekaru sun dan ja, yanzu jikoki suke yin wannan ba ma yara ba, ya kamata a ja girma, masamman ma da yake ta zama malama a wasu makarantun islamiyya. Ba ina ƙoƙarin cewa ya yi kuskure ne da har ya bar ta ta yi karatun addini bayan shi mai son rayuwa ne ba, ƙoƙarin da nake yi shi ne, tunda ko tun da can tana da ra'ayin karatun addini kamata ya yi ta canja mijin tun farko, ta sanya masa ra'ayin taimakon addini, in za su fita ta saita shi zuwa wurin da za su tafi, na sani maganin wannan cutar bai yuwuwa a 'yan shekaru ƙalilan, amma tabbas takan warke garau tare juriya da farmakin sari-ka-noƙi, amma in ya kasance kowa da abin da yake so, kuma na abokin zamansa bai yi masa ba, da wahala a sami daidaituwar zamantakewa a tsakaninsu. Amma ta nahiyar halitta kuwa wani sa'in akan sami sabani kuma ya kasance haka din shi ya fi, misali in namiji ya zama masifaffe mai yawan fada, matarsa kuma mai haƙuri ce matuƙa, sai ka ga an jima ba a sami sabani ba, kwanannan muka yi magana da wani abokina yake yaba wa wata dalibarsa cewa wai ta ce ba za ta auri yaro ba, domin tana da zafin kai, wai za ta auri babban mutum ne wanda zai iya jure wautarta, ya ce tun da ta yi auren kuwa ba wanda ya sake jin wani abu game da ita, to ban da wannan in aka sami namiji sauyar-sala, in dai matarsa tsayayyiya ce to da wahala ka ga gidan ya lalace.

Ta ɓangaren rayuwa da zabin abin da ake so kuwa, ni na fi ba da shawarar mutum ya zabi abokin zama mai ra'ayi irin na sa, ta ɓangaren abinci, sutura, makwanci, har da shimfidar ita kanta, koda yake wannan yakan yi wahala, amma namijin da yake da matsananciyar buƙata to ya nemi wace ta saba, ina nufin bazawara, in ba haka ba yanzu kowa zai ji tsakaninsa da iyalinsa, ga wani abin dariya: Na yi aiki da wata 'yar Indonesia, sai ta ce tana so na amma matsalar farko da za ta fuskanta ita ce ni baƙi ne. Ba yan mun tsallake wannan sai ta fara tambayata wai sau nawa nake wanka a rana? Na yanko na ce 2, sai ta nuna cewa to ba laifi amma ya kamata na ƙara ya kai 3, duk da haka dole na san cewa ba zan kwanta ba sai na yi wanka, sa'ata ma da ba ta kawo nau'o'in abincin da take ci ba, amma dai ta kawo wasu dogayen rigunan mata guda hudu tana son ta san irin kalan da na fi so, a ƙarshe sai ta nemi ta san ko sau nawa za mu riƙa fita shopping a wata, da kuma irin kalan man da zan riƙa siya ma ta don gyaran gashi. Sai kuma yadda rayuwarmu za ta kasance, ita 'yar ƙasar waje ce ni dan Nigeria, a ina za mu zauna, a ƙasarta gaban uwayenta ko a ƙasata gaban uwayena? In a ƙasata ne ya za ta yi wajen sada zumuntarta? Ban da wannan tana so ta ji shin sa'o'i nawa za ta riƙa samu da ni a duk yini? Dare dai gaba daya na ta ne, ta ce na shirya kuma duk in na makara za ta iya biyo ni ta mai da ni gida, babban abin dariyar a nan, wai shin aiki muke yi kawai tare, koma akwai soyayya a tsakaninmu? Sannan namiji dan Nigeria anya irin wannan rayuwar za ta tafi da shi daidai kuwa? Kuma idan ta san ina da mata ya za mu ƙare? In kuma daga baya na nuna ma ta zan ƙara aure ya za mu yi? Har ma fa ta nemi mu yanke yawan 'ya'yan da za mu haifa! Kowa sai ya san irin auren da zai dace da rayuwarsa in ba haka ba kuwa zai yi nadama ba 'yar ƙarama ba. Maza da yawa hasken fata yake tsole mana idanu, koda yake buƙatummu sun sha bamban, wani launin yake diban hankalinsa, wani kuwa ado a gaban mota, wani so yake yi shi ma ya auri jar mace kamar wane da wane, wani baƙi ne yana buƙatar ya dan sami sirkin launi a 'ya'yansa, wani kuma ya fahimci cewa auren farar mace alama ce ta arziƙi, don haka tun da ya sami dan abin masarufi to sai kuma a nemo ta, na ƙarshe a lissafina shi ne galibin mutane sun yarda da cewa mace mai farar fata ita ce kyakkyawa, kenan wanda zai auri kyakkyawar mace sai ya auri fara, su ma matan sun fahimci haka, shi ya sa wasu suke ƙoƙarin sauya launin fata, sai ka gan su kamar hankaka, sama fari, ƙasa baƙi, wannan duk ba shi ne ba, in dai ba a sami daidaituwar fahimta ba akwai matsala.

4) A baya na nemi a sami daidaituwar wayewa da ilimi, wannan kuwa don gina gaba ne, macen da take da fahimtar duniya irin maigidanta ita ta san yadda za ta taimake shi wajen raya gidan, in ba haka ba kuwa kullum za su kasance cikin sabani, yanzu dai mu waiwayi rayuwar Annabi SAW mu ga yadda Khadija RA ta taimake shi wajen cin nasarar yada saƙon da Allah SW ya turo shi da shi, ta yi amfani da ƙwaƙwalwarta har ta kai shi wajen dan baffanta Waratu bn Naufal, ta haƙura ta riƙa ƙyale shi ya kwashe watan Ramadan a kogo duk shekara, ta tura masa kudinta ya yi jihadi da su, ta bar masa mulkin gidansa a matsayin shi ne babba sai yadda ya yi, yana zuwa da sabon addini ita ce ta farkon amsa, har ta rasu ba a rawaito mana wani jidali tsakaninta da maigidanta ba, bare mu ji ga jayayyar da ta taba yi da shi, sabo da daidaituwar fahimta a tsakaninsu, shi ya sa a tarihi in dai ka fadi Annabi SAW ba sai ka kira ta ba don abu daya za ka sake fadi. A ce namiji ya ba wa mace shekaru, ko ita macen ta ba shi wata tazara ba ya nufin za su zauna lafiya ko za a yi ta tashin hankali, amma idan ya kasance ita ta yi nisa a karatun boko ko na muslunci, shi kuwa bai san komai ba, tabbas wannan rashin daidaituwar zai iya haddasa sabanin fahimta a tsakaninsu, galibin abin ma da yake hada irin wannan auren za ka taras sha'awace ba soyayya ba, ko dai ita ta so abin hannunsa, ko shi ya yi sha'awar kyawunta ya zuba kudi ya dauka, ko kuma auren dole, ko ta rasa miji da wuri ta dauke shi da haƙuri, to ba auren ne ƙarshen magana ba, wanzuwar soyayya ta har abada. 5) Zancen daidaituwar addini kuwa, mun sami labarin wata Igbara da ta auri wani Bahaushe, ta ƙi yarda ta muslunta amma kuma ta ƙi ba wa 'ya'yanta damar da za su yi sakaci da addinin babansu, yaran sun girma cikin tarbiyyar muslunci da son ibada, kenan wannan ya nuna mana cewar akwai abin da muslunci ya hango na halasta wa musulmi auren kirista mace, sai dai kuma na san wace ta koma ruwa bayan rasuwar mijin, kuma ta gudu da 'ya'yan, na kuma ji wace ba ta ma bari ya rasu ba ta kwashe 'ya'yan ta yi awon gaba da su, na ga wanda ya auri 'yar shi'a ta shi'antar da shi, shi ya sa nake ganin ra'ayin Bn Mas'ud RA da Bn Abbas game da ƙin auren ahlul kitabi (Wato Yahudu, Nasara [da Shi'a] ) abin dubawa ne sosai. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

 

Post a Comment

0 Comments