Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 31)
Baban Manar Alƙasim
Bari dai na dan rairayo miki
wasu nasihohi don jin dadin zama da saurayinki ko maigida:- a) Ki yi iya bakin ƙoƙarinki wajen rashin gaya wa
maigidanki laifuffukansa, kowani lokaci ki ce ya yi kaza da kaza, in ya saba da
haka wani zai auka miki da maganar da ba ki taba zato ba, kuma duk abin da kika
ce ya yi ba zai waiwaye shi ba, don ya saba jin makamancinsa yau da kullum, da
sannu a hankali zai yi miki nisa ba tare da kin sani ba, idan kina yafe masa
kina fadin kyawawan ayyukansa zai riƙa ƙoƙarin inganta su.
b) Ki yi ƙoƙarin nisantar zato, misali ki
ce yana yi min haka ne don na tsufa, ko don ban haifi da namiji ba, ko ki raya
cewa yana son ƙara aure ne, akwai wace take ganin ba ma ya son ta ne, duk kuwa da
abubuwan alkhairin da yake ma ta, zato ko a Ƙur'ani Allah SW ya fadi cewa
bai taba maye makwafin gaskiya, duk wani abu da kika gani na mijinki ko na
saurayi, in bai burge ki ba, to ki yi ƙoƙari ku tattauna da shi cikin
fahimtar juna, wata ƙila ya ƙumso wuta, in kina son ki yi maganinsa to ke ki debo ruwan sanyi
sai ki kashe ta, wuta ba ta kashe 'yar uwarta sai dai ta habaka ta.
c) Matsalolinki da maigidanki
ko saurayinki kar ki bari uwaye su riƙa shiga, ma'ana duk dan abin da
ya yi miki ki kwashe ki kai wa uwanki cewa ya yi min kaza da kaza, ki yi ƙoƙarin maganin lamuranki da
kanki, wasu matan don wauta hatta ƙawayensu sukan san matsalolinsu
da masu gidansu, da haka wata takan riƙa ba ƙawarta mummunar shawara har ta
banka ma ta gobara a gida, Bahaushe yana cewa: Mai daki shi ya san inda ruwa
yake zuba masa, akwai ban takaici a ce ƙawaye ne za su ba mace shawarar
yadda za ta gyara gidanta, amma na tabbata, uwa in ba ta banza ba ce ta fi kowa
cancanta da wurin.
d) Sau da yawa mu maza ba mu da
adalci, wani lokaci kuma rashin kula ne, mukan riƙa kwatanta shekarummu da
tunanimmu daidai da na iyalimmu, idan abin da muke so bai samu ba to ranar da
wa Allah ya hada mu ba da su ba? Wannan tabbas kuskure ne, amma mace sabo da
sanin halin maigidanta, zai yi kyau ta riƙa gudun abubuwan da za su
haifar ma ta da tashin hakali, takan san lokacin da ya dace ta yi magana ta
mutunci da shi, da kuma inda sam bai kamata ba, ta kiyayi abin da zai kawo ma
ta nadama. e) Idan mace tana ganin cewa namiji bai yi ma ta adalci a wasu
abubuwa ba, to kamata ya yi ta fara magana kan matsalar ne da yadda za a yi
maganinta, amma ba ta yi ƙoƙarin nuna masa cewa ita ce mai
gaskiya ba, sau da yawa maza ko ba su da gaskiya ba sa karbar kuskure, idan
mace ta rungumi kuskuren namiji yakan sani, sai dai ki ga yana neman ku
daidaita a dabarce, amma ba zai iya cewa a yi haƙuri ba, nemi kawai a kalli gaba
ban da waiwayawa baya. f) In kina da wata magana da kike so a tattauna za ki
iya gabatar da ita a lokacin da kike ganin ya dace, misali ki nemi a shiga
maganar daga wani abu da ya yi kama da shi, sau da yawa in namiji ya shirya wa
wata matsala wace ya san ita kike ƙoƙarin kawo ta, ina iya dauka ma
ta tsattsauran mataki, ko dai ya ƙi yadda a tattauna ta, ko kuma
ya auka miki gaba daya, sau da yawa maza sun san yadda za su taka wa matansu
burki, ko namiji ya fusata ƙwaƙwalwarsa tana iya tuno masa
baya, mace kuwa zuciyarta takan fi rinjayarta, hasali ma ba abin da za ta iya
matuƙar ya ƙi ba ta hadinkan da take buƙata a wurinsa. g) Idan wani abu
ya baƙanta miki rai, kika ga kuma ba za ki iya haƙuri ba dole sai kun tattauna da
maigidanki, to kar ki fuskance shi a lokacin da zuciyarki take tsakiyar
tafarfasa, ki dan bari ki sarara tukun, shi da kansa zai shirya wa abin da zai
faru, jiranki kawai zai yi ki yi magana, amma idan kika watsar shi to zai yi
la'asar, masamman idan ya ga kin watsar da maganar, ba namijin da zai ce bai
san ya yi kuskure ba, kuma ke ma in ba a cikin fushi kike ba za ki fi samun
hikimar da za ki zabi kalmomin da za ki yi magana da su, kuma tunaninki zai
koma ne ga warware matsalar da ake ciki ba tuhumar batanci. h) Maza fa suna
suka tara, amma kowa da halinsa, in za a shekara ana fadin yadda za a mallaki
zuciyar namiji wata macen za ta gaya maka cewa wallahi ban da maigidanta, kuma
in zan kwana ina bayanin nau'o'in soyayya za ka taras wata ta yi dubunsa ba
tare da wani canji na a zo a gani ba, amma sau da yawa kowace mace takan san
maigidanta, shawarata kawai macen da ta sabar wa kanta da taushin zuciya,
daddadar magana, zazzaƙar murya, iya kwaliya da
kwanciya, kwarkwasa da kisisina, iya abinci, takan fi dadin zama zama da wata. A
nan zan dakata. Sai mun haÉ—u a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.