Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 30)
Baban Manar Alƙasim
d) Ya kamata mace ta zama mai
natsuwa, masamman lokacin da ranta ko na mijinta ya baci, a duk lokacin da ran
mutum ya baci, 'yar matsalar da ko ƙaramin yaro zai iya warware ta
sai ki ga babbar mace ta gaza maganinta, ƙila ma abin da ya sa Annabi SAW
ya ce wa wani kar ya yi fushi kenan lokacin da ya nemi ya yi masa wasiyya, in
mace ta yi fushi za ta bata abubuwa da yawa; Alaƙarta da maigidanta ba ƙara kyau za ta yi ba, sannan ga
abin da diyoyinta mata za su kwafa, kamata ya yi ta yi aiki da ƙarfin zuciyarta ta yi murmushi
a gaban 'ya'yanta duk lokacin da ranta ya baci. e) Yakan zama wajibi ga mace ta
zama taskar adana sirrorin maigida, a bayyane yake namiji bai da wani mahaluki
da ya fi kowa kusa da shi sama da iyalinsa, alokacin da ya gama gamsuwa da
dabi'unta, cikar hankalinta, amanarta da adalcinta da wahala ka ga yana
kame-kamen wanda zai rufa masa asiri, ko wanda zai yi sirri da shi sama da
matarsa a cikin gida, yanzu ita ya kamata ta ba shi wannan cikakken amincin, ta
wajen ma'amalolinta da shi, ko da 'yan uwansa ko na ta, ko ma wasu mutanen na
waje, haƙiƙa kwadayi, wayau da son kai su ne a gaba-gaba wajen rushe gamsuwar
namiji da iyalinsa. f) Wasu matan su suke ƙarfafa mazajensu a kan ibada,
na ga wata matar da ta raba maigidanta da shan giya cikin dabara da hikima,
wata kuma ta hana na ta zina, ga shi Rumasa'u ta musluñtar da Abu Talha, akwai
matan da suke sanya mazansu sallar jam'i, ko fita sallar Issha da ta Asuba,
akwai ma mai ƙarfafa mijinta a kan ƙiyamul laili, na taba yin
zamani da wani mutum da ya ce min iyalinsa ta koya masa karatun baƙi, ita take nuna masa yadda zai
karanta Ƙur'ani, ko ba a gaya maka ba ka san zama yi kyau ai ko? In mace ta
zama mai addini ita ce Annabi ya ce a aura, tabbas 'ya'yanta ma haka za su
kasance.
g) Sannan mace ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen mantawa da
rayuwarta ta gida, ta san cewa wannan sabuwar rayuwar da za ta shiga ko wace
take ciki ita ce rayuwar da Allah SW ya zabar ma ta, ba dole ba ne ta sami jin
dadi kamar na gidanta, haka zai yi wahala a ce ta dara duk ƙawayenta more zaman aure, gida
da mota ko sutura da abinci da sauran kayan more rayuwa Allah ne yake ba da su
ga wanda ya ga dama, in mace ta yarda cewa dan ƙwan da maigidanta zai ba ta ya
fi ragon da mijin wata zai siya wa iyalinsa ta huta, galibi yawan hange-hange
yakan hana mace zabin miji na gari, in ma ta yi auren takan kasa natsuwa ta
mori rayuwarta da shi. h) Wasu matan sukan yi sha'awar a ce su ne suke juya
gidansu kamar yadda suke so, Annabi SAW ya fadi cewa al'ummar da ta sanya mace
a kan jagorancinta ta gama lalacewa, haka ko gida ne aka ce mace ce ke juya shi
ba wani abin arziƙin da za a iya ƙullawa, ko neman aure ne wani
ya shiga, in dai aka ce yarinyar 'yar mace ce to da wahala ka ga ya ci gaba, na
taba ganin matar wani soja da fasinjoji suka yi ta yi ma ta Alla-wadai, sabo da
raina maigidanta da ta yi a tasha, kafin mu shiga mota, bayan mun sauka kuma na
ji mata suna ta yi ma ta tir, wai tana daga wa mijinta murya a kasuwa, duk
matar da mijinta yake tsoronta to ta dafa kai ta yi kuka.
i) Wasu mata sukan yi babbar kuskure a kan kishi, wata gwara maigidanta ya rasa lafiyarsa ko su zauna cikin talauci da a ce maigidanta ya yi ma ta kishiya, na ga wace ta sa aka kori mijinta a wurin aiki don kawai ta baƙanta masa rai kamar yadda shi ma ya baƙanta ma ta, na ji wace take roƙon kar Allah ya yi wa mijinta arziƙi don dai kar a yi ma ta amarya, kamata ya yi mace ta so ci gaban maigidanta a kowani hali, ta taimaka masa da tunaninta, da ƙarfinta da dan abin da take da shi na kudi, wannan har abada ba zai manta ta ba, ai namiji yakan saki mace ya je ya yi ta yi ma ta kuka da hawayensa don ta dawo. j) Bisa al'ada wajen neman aure a ƙasar Hausa ko ma na ce a wannan nahiyar ta mu ta Afurka mukan bari sha'awa ta yi mana mummunan tasiri a lokacin neman aure; son ganin juna, jin muryar juna, ƙaunar gwamatsuwa wuri guda da dai sauransu, yadda ita za ta riƙa miƙa masa duk sha'awar da yake buƙata, shi kuma yana bakka ta 'yan sulalla da sauran hidindumu, da yake sha'awace zalla kuma yanzu an yi aure buƙatu duka sun biya, dole a nemi sha'awar kamar yadda take da a rasa, to ke in kika nemi canjawa wai don shi ma ya canja ba shakka za ki yi nadama ba 'yar ƙarama ba. k) Duk lokacin da mace ta amince wa kanta cewa ita mataimakiyar namiji ce ta huta, kamata ya yi ta karance shi ta san yadda za ta riƙa bullo masa, kar ta yarda ta riƙa samun sabani da shi, duk lokacin da ta wahala domin maigidanta ta fi samun hutu a wajensa, a sa'in da ta yarda cewa ita baiwarsa ce nan da nan za ta mallake shi, in ta kau da kanta daga dukiyarsa sai mallaki duk abin da ba ta zata ba, in da za ta amince wa maigidanta cewa shi ne komai to a ƙarshe sai yadda ta yi da shi, wannan ma ya tuna min, bari zan ba ki wasu shawarwari masu tsada. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.