Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 32)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alqasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 32)

Baban Manar Alƙasim

To bayan mun waiwayi abubuwan da suka wajaba a kan maigida, muka sake duba wadan da suka wajaba ga uwargida, zai yi matuƙar amfani kuma mu duba wadan da suka wajaba a kansu su biyu:- 1) Ta kowani hali yakan wajaba ma'aurata su duba kawunansu, kuma su amince wa kawunansu 'yan matsalolin da kowanne a cikinsu zai iya aukawa, namiji ya san shi babba ne, Hausawa sukan ce "Babba juji ne" juriya dama ta wajaba ne a kansa, ita kuma ta yarda cewa ita mataimakiya ce, amma maigidanta shi ne shugaba, da wannan za a iya maganin abubuwa da yawa. Domin warware wannan tankiyar bari na gaya maka wani abu:-

a) Nakan ga hotuna suna yawo wai namiji yana ba wa mace furanni, ko kuma ya fasa ƙirjinsa ya ciro zuciyarsa ya miƙa ma ta, wannan kuskure ne, mace ita ce take nuna wa namiji ƙauna ta ƙarshe, take sauke masa abubuwan da suke damunsa, ta hanyar mantar da shi su da soyayyar da take nuna masa, hoton da ya ba ni sha'awa shi ne wanda namiji ya zama wa mace gado ta kwanta a kansa tana barci, ko wanda ya zama ma ta gada ta taka ta wuce, don ba za ta iya tsallake rami ba.

b) Ita mace babban abin da za ta yi shi ne duk zafin da namiji ya shigo da shi ta sauke masa, in ransa ne a bace ta faranta masa, in ya dawo a matsayin mabuƙaci ta gamsar da shi, ya zama dai ba wani abin da za ta bari ya ƙuntatu da shi, bare har ya nemi taimakon wani ba ita ba, ita ce matattarar rayuwarsa, kuma manajan gidansa, in ƙauna ta ginu a tsakaninta da maigidanta da wahala ta riƙa kallon abin da ta yi wa maigidan a matsayin ta taimake shi, ko tana buƙatar ya gode ma ta, babban abin da za ta buƙata kawai shi ne ta nemi sani ko ransa ya yi masa dadi. d) Ya zama cewa in namiji ya yi wa mace kyauta kar ya riƙa ganin kamar ya ba ta duniya ne da abin da yake cikinta, ya sanya a zuciyarsa cewa ya yi wani abu ne da ya zama wajibi a kansa, kuma in har bai yi ma ta ba to shi ne ya gajiya, kenan in ta gode masa ta kyauta, in kuma ta manta to da ma bai zama dole a kanta ba, wannan ba zai rage komai ga abin da yake da niyyar yi nan gaba ba, kenan ma'aurata matuƙar abubuwan da za su aikata don jin dadin juna ne, to kar su jira dayansu ya gode musu, don in ka yi wa kanka abu wa za ka jira ya ce ma ka ya gode? e) Tsakanin namiji da mace ba wanda za ka samu cikakke, don haka in namiji ya gano cewa matarsa tana da rauni ta wuri kaza, kamata ya yi ya ƙarfafa ta, ba wai ya ruguza ta gaba daya ba, don ya nuna wa duniya cewa yana ƙaunarta, kamata ya yi ya nuna cewa shi ne fa maigidanta, don haka ne ma suka je sheda cewa lallai sai ta zama matarsa, sai ta yi masa hidima, kuma sai ta zama uwar 'ya'yansa, in da kuma ya gan ta da ƙarfi sai ya ririta shi yadda za a dade ana amfana da shi, haka ita ma macen in da ta ga baraka a gidan mijinta sai ta yi ƙoƙari ta rufe, don sirrin maigidanta na ta ne, in asirinsa ya rufu na su ne gaba daya ya rufu in da ya tonu to daga ita har 'ya'yanta ba mai ganinsu da daraja, wannan shi ne sirrin dinke gida, duk lokacin da mace take ganin ita ce maigidan, shi ma goje yake jin kamar shi ne kowa na gidan to matsala ta ƙare.

f) Akwai wani babban abin da za mu koya daga Annabi Ibrahim AS, domin shi ne ma ya rada mana suna musulmai, yadda ya roƙi Allah ya kare masa iyalinsa da zuriyarsa, daga cikin addu'o'insa ne ma ya roƙi Allah da ya sanya ƙauna a tsakanin matansa da zuriyarsa, ya sanya su su zama shugabannin al'umma, tabbas Allah ya amshi addu'arsa, don Annabawan bayansa duk tsatsonsa ne, kuma masu juya duniya da masu riƙo da addini sosai a dauri ko a yanzu duk dai daga cikin diyoyinsa ne, da wannan za mu fahimci cewa; yi wa masu gida addu'a, ko su uwayen gidan abu ne mai matuƙar girma da daraja, gami da taimakon kai da kai. g) Wasu lokutan wasu abubuwa sukan bayyana ne kawai bayan daura aure, misali: Duk namijin da zai nemi mace yakan so ne ya ribaci zuciyarta, idan ita mai son zuwa islamiyya ce ko makarantar haddar Ƙur'ani sai ka ga saurayin ya shiga sanya jallabiyya da hula, ko ya dan bar gemu, da ta dan yi magana ya ce "Subhanallah" da dai sauransu, in kuwa 'yar duniya ce sai ya canja kama, hatta maƙiya sahabban Annabi, wato masu ƙaryar ƙaunar ahlul baiti, yadda suke yi kenan su aure 'yammatan muminai, to in irin wannan aibun ya bayyana, in dai ba na aƙida ba ne kamar babbaƙu, ina ba mace shawarar ta yi lissafi mai zurfin gaske kafin ta kai ga yake hukunci, ta yi masa kallon da likita yake yi wa maras lafiya, ba wai ta ce bai da amfani a rabu da shi ba. Sai ta yi ƙoƙarin gyara shi ta yadda zai amfane ta ya amfani 'ya'yanta, sai dai in abin ya shafi aƙida, haka namijin da mace ta boye masa aibinta, misali ita tsohuwa ce ta yi ta fito masa a yarinya, ko baƙa ce ta canja launi, da dai sauran abin da shi ba zai so gani ba, kamata ya yi shi ya yi tunanin cewa ita ya aura fa ba jikinta ko kalarta ba, kuma ita din dai ce yanzu ba wata ba, kar ya bari shaidan ya kunyata shi a gaban masu hankali har ya zubar da ƙimansa a gabansu, ya yi iya abin da zai iya don ganin ya girmamata da soyayyar ta yake fadi a gabanta ba sha'awar da ya boye a zuciya ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Post a Comment

0 Comments