Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 23)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 23)

Baban Manar Alƙasim

Kafin mu je ga maganar inda ya halasta mumini ya kalla, ya kamata mu dan waiwaya wurin wadan da suke fassara kansu da sunan cewa su masoya ne da suke son su yi auren soyayya, a maimakon su kalli ɓangaren addini sai su koma kwaikwayon Turawan Yamma, uwayen yarinya su yi biris da 'yarsu tana bibiyar wani namiji, baligi, ta kebe da shi, wata ƙila ma har a dakinsa, 'yan birni ma sukan tafi silma, filin wasa, da gidajen shan iska da sunan soyayya, wata ma har barin garinta takan yi wai ta tafi wurin masoyi ko inda za ta sha soyayya da shi tunda an gama komai shi ne zai aure ta. Wallahi ni da idona na ga wasu da suke kirar kansu masoya, sun tafi bakin kogi, shi ya tube daga shi sai dan kamfai, yana wanka, ita kuma ta tsaya a bakin ruwan wai tana riƙe masa suturarsa, sun gama soyewar amma sai ta yi ƙurmus, don bai sami damar aurenta ba, abin da nake gani game da wannan ya kamata ne ya binciki dabi'unta in zai yuwu ya aure ta, ita ma ta binciki na sa in zai yuwu ta zauna da shi, amma uwaye su bar balagaggu kullum ana motsa sha'awar juna, wannan yana nufin sun tabbatar da cewa Shedan ya mutu kenan, ko ba su karanta ba sun taba jin har Annabawa SA bai ƙyale ba bare wadan da ya san ba su da wata kariya ta masamman.

Sakaci irin wannan babu ko shakka takan zo da mummunar ƙarshe a wasu lokutan, kuma uwayen yarinya za a zarga da tura diyarsu cikin matsalar da za ta ragargaza 'yammatantakarta, ta bata ma ta suna, wai ma ba haka ba, ya za a yi in saurayin barawo ne? Ko mayaudari ne? Abin haushi za ka taras namiji har fadi yake yi cikin izza cewa aurensa kaza, kuma da zai sake nema tabbas za a ba shi, wani an san cewa ko aurensu ba ya yi bare ya sake su, amma da zarar ya nema sai ka ga an bar shi da yarinya kullun dare wai yana zance, kwanaki na ga wasu suna rikici, ya auri yarinya da wata shida ta haifi lafiyayyen yaro, sun ce wai ya gama cika watanninsa. Abokansa suka same ni da wannan maganar sai na ce musu "Su ji tsoron Allah, don yarinyar ta ce ba wanda ya taba taban jikinta sai shi, shi ma ya yarda da haka, amma shin saninta din kafin aure ne ko bayansa?" To da yake akwai malami a kusa da mu sai na ce su je su tambaye shi, don suna shakkar cewa an daura auren ba ta yi istibra'i ba, wasu kuma suna ganin an daura auren tana da ciki wata 3, shi ne ma ya sa aka yi gaggawar daura auren kar a ji kunya, duk dai zato ne ba a tabbatar ba. Wani ya ce

"Abin fa dole a yi tunani, bayan bacin suna na cewa sun yi zinace-zinace kafin daura aure, sai kuma a ce dansu na farko an same shi ne ba a aure ba?" Sai na ce " To in ana tunanin hakan amma aka boye ya matsayin sauran 'ya'yan da za su biyo baya?" Duk dai rashin kamun kai ya jawo haka, ya zama dole a kan uwayen yaran, wato shi manemin da wace ake nema su yi ƙoƙarin samar wa diyoyinsu dauwamammiyar zamantakewa, su samar musu da tsarkakakkiyar soyayya wace za ta yi ta ci gaba a tsakaninsu, ba mai ƙarewa bayan saduwa ba, in an yi haka to an yi ƙoƙarin yin riƙo da hukunce-hukuncen addini, ta wurin taimakon yara masu tasowa. Duban mace kafin a aure ta ya tabbata daga Annabi SAW, amma zancen zaman hira da daddare da matasa suke yi a cikin duhu jiki na gugar jiki, ga magana cikin sanyin murya da 'yan ƙananan dararraku na motsa sha'awa, su kuma me ake nema da su, kuma wa ya kawo? Malamai dai sun yi ta yin bayanai kan ina za a duba, har ta kai ga wani yana tunanin duk jikinta zai duba kafin ya fara nemanta, koda yake wannan da dama cikin malaman sunna ba su yarda da shi ba, sabo da hatsarin da yake tattare da haka, kuma ba a sami nassi fayyacecce daga Annabi wanda ya nuna haka ba, hasali ma akwai hadisai da dama da suka nusar wajen gudun kallon al'aurar matar da ba ta halasta ba. Sai dai na ga wani abin da ya ba ni sha'awa a wata ƙabila ta larabawa, in ka zo neman diyarsu za su sanya ta ta kawo maka matsattsen lemo, daga ita sai wani shimi (dress ne maras hannu da yake ƙarewa a gwiwa) ta ba ka ta zauna tsawon gaisuwa da za ta yi, sai ta koma ta sanyo cikakkiyar sutura, kai da sake ganin fuskarta ko wani bamgare na jikinta kuma sai a gidanka, ko ka zo sai dai ta zo ta gaishe ka kawai ta koma, in wata magana kake da ita sai ka gaya wa uwayenta ko 'yan uwanta, wannan kam a wurina ya yi, don wani Ustaz ya taba gaya min cewa shekararsa 3 yana neman matar da ya aura, amma sau 3 kacal ya taba zaman zance da ita, shi ma din a gidan mahaifanta, kuma da rana ba wanda ya kai minti 30.

Abin ya ba da sha'awa ƙwarai, ashe ko a nan Nigeria akwai uwaye masu sanya ido sosai a kan diyoyinsu, Nawawiy RL yana cewa a sharhin Muslim game da hadisin ganin mace kafin a aura: An halasta duban hannu ne kawai da fuska, don fuska tana nuna kyawunta ne gaba daya, hannu kuma yana nuna laushin fatarta da lafiyarta, malamai ba su shardanta cewa sai ya nemi yardarta a kan haka ba, yana iya satar dubawa a lokacin da ta yaye ba ta ankara ba, ba sai ya ce zan duba ba, ko ya ce "Na fa duba kaza da kaza". _A wani hadisi na Abu Dawoud da Hakim ya inganta shi, Annabi SAW ya ce " In dayanku zai nemi mace, matuƙar zai iya duban abin da zai janyo hankalinsa zuwa ga aurenta to ya yi. Kenan dai mislunci bai haramta duban mace kafin a aure ta ba, sai dai ina ne ya halasta a duba din? Ba kamun kai ba ne mace ta hana namiji sanin kyawunta da lafiyarta da hujjar sai ya aure ta, haka ba Shari'a ba ce ta bude masa jikinta ko kullum ya yi ta kallo da sunan masoyi, asali a addini shi ne tsakaitawa a dukkan komai._ A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

 

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 23)

Post a Comment

0 Comments