Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 19)

    Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  19)

    Baban Manar Alƙasim

    Tambaya: Shin dole ne a sha soyayya a lokacin neman aure don samun danƙon zamantakewa, ko soyayyar bayan aure ita ta fi? Amsar wannan tambayar takan koma bayan fahimtar ma'anar soyayyan ne, idan soyayya ta ba da ma'anar karantar juna hade da kyakkyawar ma'amalla da sake wa juna jiki, kwadayin faranta wa juna da taimakawa ta kowani hali ba tare da buƙatar sakamako ko kallon cewa mutum ya yi abin da bai zama dole a kansa ba, gami da ƙoƙarin rufe sirri to ba zai taba yuwu ta samu ba dole sai da aure, amma in ta tsaya a kan jin sauti da son ganin juna kawai ba ko shakka za ta iya samuwa tun gabanin daura auren ma. Idan mutum yana gaya maka ma'anar aure sai ka yi zaton yana fassara maka ma'anar soyayya ne, sai dai in ka yi nazari kan abin da samari suka dauki ma'anar soyayya a yau sai ka gane cewa akwai bambanci, amma tabbas a aure akwai masayar alaƙa a tsakanin bangarorin guda biyu, domin tabbatar da wannan alaƙar dole a sami dauwamammiyar ƙauna da tausayi a tsakaninsu, da kulawa gami da fahimtar juna da gamsarwa, ta yadda ba a gane cewa ba wannan matuƙar akwai wancan. Irin abin da muke ƙoƙarin fadin ya wajabta ga masoya na gaskiya (wato ma'aurata), shi ne bai iya yuwuwa ka nuna ƙaunarka ga masoyi sai ka yi ƙoƙarin tace dabi'unsa, gyara aƙidarsa da sauran ibadunsa, kiyaye tunaninsa da tsarkake shi, inganta abincinsa, kyautata suturarsa da matsuguninsa, rufa asirinsa, ƙarfafa zumuntansa da kuma zama magani ga duk wata cuta da zai iya kamuwa da ita, ta jiki ce ko ma ta yanayi ko ta aljuhu, to in dai haka ne, ƙarya ake yi a ce akwai wani aure na mintuna ko wasu sa'o'i, kai dai a ce ana son yin zina kawai, ko kuwa ba wa wasu ƙofar aikatawa don a ribaci aƙidarsu, shi ne ma a darasin baya muka ga kashedin da Annabi SAW ya yi mana a kan haka don mu kiyaye.

    Babban abin da yake danƙwanta zamantakewa ta yadda kowa zai yi matuƙar ƙaunar dan uwansa har ya kai ga shedawar samuwar soyayya ta gaskiya shi ne: Kowa daga cikinsu ya riƙa ji a jikinsa cewa ba zai iya rayuwa ba tare da dayan ba, ta wurin nuna masa a aikace ba surutun banza a baki ba, in dai ina yin komai don ganin na tabbatar da rayuwata gare ka, kai ma kana yi don tabbatar da rayuwarka gare ni, ba na tsammanin wani shaidani na mutum ko na aljani zai sami barakar tarwatsa wannan rayuwar, amma soyayyar baki ko ji a zuciya kadai wannan sha'awa ce kawai ba ta cika samuwa a matattarar Hausa/Fulani bayan aure ba. Soyayya a cikin aure, ko na ce rayuwar auratayya:-

    1) Ba a bu ne na wani da yake boyuwa a zuciyarka ba, wanda kake jin zai iya sanya ka ka ba shi abin da yake so ko ka yi masa abin da zai faranta masa rai, kai din ne kacokan na sa, da zai yi amfani da kayansa a duk lokacin da yake so da kuma sifar da ya ga dama matuƙar bai saba addini da dabi'a ba, in ya zamanto shi ma haka yake kamar yadda kake to za a sami cikakken masayar ma'amalla, kenan ba za mu ko tabo auren dole ba, ga wanda yake son ya yi rayuwar jin dadi, namiji ne shi ko mace.

    2) Soyayyar aure ko zamantakewarsa ba ginanne ne a kan abu kaza ba, misali kyawun mace, ko kudinta ko matsayin babanta ya sa ka aure ta, gamsuwa ce irin ta zuciya wace ba ta da musabbabi sama da cewa wane na wa ne, ni ta sa ce, takalmin kaza mutu-ka-raba, ina son sa a kowani zarafi, na samu ko na rashi, don haka ban da wanda ya wuce shi, wannan ya sa sau da yawa soyayyar mace ta fi ta namiji zama gaskiya, don ita tana zaune ne kawai ka ce kana son ta, ba tare da duba komai ba ta fara saurararka, har a hankali ta yanke shawarar ta miƙa maka wuya, daga bisani ta san ko kai waye, me kake da shi, wata ma har auren dole ake yi ma ta kuma ta riƙe mijin gam, har ma ta yi kishinsa, kakannina mata ma ce min suka yi ba su san mazajensu ba sai bayan buden kai, kenan har sun kwana da su ba su ma san fuskokinsu ba.

    3) Soyayyar aure abu ce da ta ginu a kan amsar rayuwar juna har abada, don haka dole a riƙa yi wa juna hanzari, aka ce harshe da haƙori duk da kasancewarsu a kowani lokaci akan saba, to bare namiji da mace masu nau'in halita da dabi'o'i daban-daban, hanyoyin tunani da na gudanar da rayuwa mabambanta, hatta fahimtar magana ko hangen nesa ba daidai namiji yake da mace ba, kenan dole kowa ya riƙa yi wa dan uwansa hanzari, ko da an sami rashin jittuwa na wani lokaci, in aka kalli matsayin mutum a rayuwa sai a mai da lamarin ba komai ba, masamman halin zamantakewa dole kowa yana da buƙatar dan uwansa a kowani lokaci, rasa shi kuma na dan lokaci ya kan yi tasiri ba dan ƙarami ba. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

     

    Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  19)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.