Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 18)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  18)

Baban Manar Alƙasim

Sheikh Gazali RL ya kawo wata Ƙissa kan yin wasa da mazakuta a littafinsa na Ihya'u Ulumiddeen 4/98, yake cewa: Wata rana mutane suna zaune a makarantar Ibn Abbas, sai wani ya ci gabà da zama har sai da Ibn Abbas RA ya ce " Ko akwai wani abu ne?" Ya ce " I, ina son na dan tambaye ka wani abu ne amma na ji kunyar mutane, to yanzu kuma ina jin nauyinka, ina ganin girmanka" sai ya ce masa " Ai malami yana matsayin mahaifi ne, duk abin da ka san za ka iya gaya wa babanka ka fado shi kawai" . Ya ce " Ni saurayi ne ban kuma da mata, sannan ina tsoron zina, sau da yawa nakan yi wasa da gabana ne na samu na fitar da maniyyi, ko akwai laifi kan haka?" Sai Ibn Abbas ya kawar da kai, can sai ya ce " kai tir! Auren baiwa ai ya fi maka, auren baiwa ya fi zina, ka auri wace za ta kare ka ya fi ka bar kanka ga Shaidan. Wanda Allah ya ba lafiya ya yi ƙoƙari ya yi aure, wallahi 'yammata da zawara da dama suna son aure amma samarin sun ƙi ba su dama, wata ta same ni take cewa don Allah na samar ma ta da mijin da zai rufa ma ta asiri ya kare mutuncinta, kowa ya san wannan ba abu ne mai sauƙi a wurin mace ba.

To ta ina za ka bar matar kirki da kai take so ba kudinka ba, ta yi maka hidima kai da yaranka, ta gyara maka zumuntarka, ta rufa maka asiri, amma ka koma kana holewa da 'ya'yan jama'a ko ka kama takin hannunka? Koda yake likitoci da dama sun ƙaryata cewa takin hannu yana kawo matsalar mazakuta, mace kuma yana rage ƙarfin matantakarta, sun ce ba ya sa komai, sai dai in ya yi yawa yakan kawo sanyin mutum, to me aka yi kenan? Duk abin da ka ji shari'a ta hana tabbas ba ka rasa shi da matsala, mafita a wannan bala'in kawai mutum ya yi aure, yana ma iya jifar tsuntsu biyu da dutse daya.

4) Abu na gaba kuma shi ne harkokin ciki, tsaftar gida da makwanci, da wanke-wanke da samo hanyoyin hutu da sauransu, ban da wannan ma, in da mutum zai rasa samun sha'awar takin mace, babu ko shakka zaman gida shi kadai zai dame shi, in da kuma a ce bai da matar da za ta riƙa kula da shi, da aikace-aikacen gida sun gallabe shi, da yawa cikinmu maza ba ma iya ko kau da kwanon da muka ci abinci, ya kake ganin zuwa cefane, dahuwa, da wanke-wanke?

Ga shara da tsaftar daki, kowa dai ya san yadda dakin samari yake, bar batun ƙazanta da sauransu ko tsarin inda za a ajiye kaya babu, Allah sarki aure zuma. To wanda zai nemo kayan abinci ya zo ya gyara ya dafa, ya wanke kwanoni, gami da tsaftar daki da ban-daki, yaushe ya ga lokacin neman ilimi ko aiki? Mace ta gari za ta iya mantar da shi komai, ta ma taimake shi gudanar da abin da ya shafi addininsa, Abu Sulaiman Addaraaniy yake cewa: Mace ta gari ba a lamuran duniya kawai take amfanarwa ba, za ta gama maka na duniyan ne don ka sami damar yin na lahiran, ga aikin gida, ga kawar maka da sha'awa, (ga kuma dimbin lada, duk ba ko kwabo, sai ma albarka iyayenta za su riƙa dura maka, a ƙarshe ta zuba maka 'ya'ya ta yi maka tarbiyyarsu, duk wahalar da za ta sha 'ya'yan dai naka ne, shi ya sa mahaifinta ya cancanci ka girmama shi.

5) Aure yana koyar da mutum abubuwa da dama, masamman shugabanci, yadda mutum zai zama sarki a cikin gidansa, ya koyi haƙuri da mace da dabi'o'inta, ya jure wa cutarwarta, ya dage wurin kyautata ma ta, da koyar da ita abubuwan da suka dace, ya yi ta neman halas don ciyar da ita, ga kuma tsayuwa a kan 'ya'yayen da ta haifo su, babu shakka matsayin aure ga dan adam bayan biyan buƙata abu ne kuma mai girman gaske, don shi hanya ne na bauta, ga dadi, kamar dai zuma, ga zaƙi ga magani. Umar RA yana cewa " Ba abin da zai hana aure sai matsalar mazantaka ko fajirci" gaskiya ne, matan halas ga su nan ko'ina, in wannan ba ta yi ma ka ba wancan babu ko shakka za ta yi, Junaid RL yana cewa "Nakan buƙaci saduwa da mace kamar yadda nake buƙatar abinci" in mace ba ta yi maka komai ba amma ta hana zina ba laifi, gaskiya ta yi ƙoƙari, to sai dai sha'awa ba wurin namiji kadai take ba, mace ma ta fi namiji sha'awa, kawai dai Allah ya zuba ma ta kunya ne, don haka wajibi ne maza su aure su kafin shaidanu su hole da su. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  18)

Post a Comment

0 Comments