Wannan na É—aya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar AlÆ™asim ya rubuta.
Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 17)
Baban Manar Alƙasim
Aure yana da fa'idodi da daman gaske, mu dai za mu
dan gutsura kadan ne kawai mu fadi, sauran sai a saurari karatun malamai:- 1)
Babban maƙasudin yin aure dai shi ne zama a doran ƙasar da Allah
SW ya turo mu, hikimar da ke cikin haka ita ce mu yawaita ta hanyar da Allah SW
ya tsara mana, yin hakan kuwa yana daya daga cikin ababan da ake bauta masa da
su, to amma babbar hanyar da za ta tunkudo mutum har ya kai ga saduwar da za a
yawaita din ita ce sha'awa, sai dai musulmi a kowani lokaci yana buƙatar mace ta ƙwarai wace za
ta kula da shi da kuma 'ya'yansa. 'Yar mutu'a ko na ce mazinaciyar da take
holewa da kowa ba ta a cikin mata na gari wadan da suka kame kansu domin mutum
guda, domin tun asali babu buƙatar tara zuriya a alaƙarta da namiji,
babu wata soyayya sai dai biyan buƙatar sha'awar
saduwa, shi kansa namijin bai da wata buƙata ta ya mai
da ita uwar 'ya'yansa da za ta riƙa jingina kanta
gare shi, mai yin aure don Allah da son kasantuwa da masoyi shi ne Allah SW
Yake magana a kansa. In mun duba wata aya a Ƙur'ani Furƙan 74 zamu
taras ma'anarta tana nufin:- Wadan da suke cewa "Ubangijimmu ka sanya ƙaunar junammu a tsakanin matammu da zuriyarmu, ka
sanya mu shugabanni ga masu tsoron Allah".
A wani hadisi ma Annabi SAW haka ya ce:- Ku yi aure
ku hayayyafa, haƙiƙa zan yi alfahari da ku a kan sauran al'umma ranar ƙiyama._ Kenan
akwai buƙatar ƙaruwa da kuma
hayayyafar amma ta hanyar da Allah SW ya tsara wa bayinsa. 2) Sai kuma kare kai
daga shedan da kuma hanyoyin da yake bi wajen yaudarar bayin Allah, tabbas
yakan yi amfani da sha'awa, mutum in dai lafiyarsa lau, namiji yake ko mace
Allah ya riga ya sanya masa sha'awar kinin halittarsa ba yadda zai yi, dole sai
ya buƙace shi, amma idan ya kasance nasa ne zai iya
amfani da shi a kowani lokaci shi kenan matsala ta ƙare, aure shi
ke halasta wa namiji mace a gaban kowaye, ya halasta wa mace namiji, in ba haka
ba sai a fada tarkon shedan, Annabi SAW ya ce wa mata "Ban taba ganin
wadan da suka gaza a hankali da addini sannan suke da ƙarfin rinjayar
gwarzon namiji kamarku ba". Tabbas namiji a hannun mace yake sai dai in ba
ta yi niyyar kama shi ba, ko kuma shi din bai da lafiyar da za ta sanya shi ya
yi sha'awar buƙatarta, amma aure garkuwa ne da zai iya hana Shedan
ya auka wa mutum ta wurin yin amfani da mace, Annabi SAW yana cewa: Ban bar
wata fitina a bayana wace ta fi cutar da maza kamar mata ba. Mace ce za ta gama
zagin namiji wai ya sanya ma ta ido, alhali da za ka dube ta sai ka ga ta gama
cika rukunan sha'awa wadan da dole namiji ya kalle ta din, ba macen da ba ta
san sirrin daga sha'awar namiji ba sai dai ko budurwa, budurwar ma ba duka ba. Da
wannan Annabi SAW ya ba da maganin kawar da wannan mugunyar sha'awar ya ce a
hadisin Muslim:- Idan dayanku ya ga wata mace ta ba shi sha'awa har ta kutsa
zuciyarsa to ya koma wurin maidakinsa, don tana da abin da wancan take da shi.
Ke nan aure ya zama magani kenan, wanda bai da shi
kuma zai fara neman wata hanyar don kawar da sha'awarsa Allah ya kyauta, Shedan
kam yana aiki da sha'awa a tsakanin matasa wajen cimma manufarsa, amma aure
yakan taka masa burki sau da yawa. 3) Ba ko shakka zaman hira, da 'yan wasanni,
ko kallo, sukan dan hutar da zuciya, su ƙarfafa mutum a
kan ibada, koda yake akwai buƙatar sanin wace iriyar hira, wasa ko kallo din,
dukansu akwai na halas da ake samun lada da na haram da ake samun zunubi, ba
kuwa a aikata sabo don a sami lada, a cikin masu kwadaitar da auren budurwa na
ji wani malami yana cewa:-
Auren budurwa (Wato ko yarinyar da ba ta gama sanin
namiji ba, irin sakin wawannan ko wace mutuwa ta yi ma ta ba kan zata) ya fi
lada, domin takan yi wasa da mijin, ga wata iriyar kissa ta ƙaramar yarinya
me saye zuciyar namiji ta sa aikata sunna cikin gaggawa, ga 'yan dararraku da
manne wa namiji, sannan koyar da ita da yake yi kullum, da ƙoƙarin
tarbiyantar da ita, ga haƙuri da wautarta duk lada za ka samu. Yasir Ramalan
Gwale (Allah ya ja kwana da aiki na gari) ya taba ba mu labarin wani dattijo da
ya auri ƙaramar yarinya, (me yuwuwa yana ta saƙar yadda zai fito
ma ta ne, kasancewarta ƙarama, kar ta yi masa kallon tsohon banza, a
maimakon wanda yake ƙoƙarin aikata sunnar Annabi don neman lada), dattijo
yana kishingide kamar yana barci, ai sai amarya ta gaza haƙuri ta bi kadin
haƙƙinta, ji kawai
ya yi ana ja masa tazuge, gari na wayewa ya nemi diyoyinsa mata duk su fidda
miji, don wace yake ganin ba ta san komai ba ashe malama ce. A nan zan dakata. Sai mun haÉ—u a rubutu na
gaba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.