Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 15)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  15)

Baban Manar Alƙasim

Aure ba abin wasa ba ne bare a yi sakaci da shi, in ba mutuwa ba akwai tsufa, duk lokacin da mutum ya yi jinkirin yin abu a lokacinsa tabbas zai yi a wani lokacin da ba a buƙata, in ba a yi sa'a ba sai ka ji ana inda-inda a ƙarshe, don ƙarfin mutum ya yi ƙasa, ga iyalinsa lokacin take ganiyar buƙatarsa kenan a shimfida, ga kuma yaransa ƙanana ne su kansu buƙata suke yi bare mutum ya sa rai da za su tallafa masa ta wani ɓangare, wannan muna maganar shimfida ne da na sauran rufin asiri, in kuwa muka juyo kan ilimin yara, kowa ya san da matsala, kudin makaranta kawai ya ishi mutum rigima, don haka auren wuri yana dab ne da ya zama wajibi ga duk wani mai idon da yake kallo. Annabi SAW ya fadakar da mu a wani hadisi na Muslim da Ibn Maja, yake cewa: Duniya ababan jin dadi ne a cikinta, mafi girmansu kuwa shi ne samun mace ta gari.

Duk lokacin da mutum ya tashi neman aure sai ya dubi inda hankalinsa zai kwanta, ba wani jin dadi a tashin hankali, wanda zai yi aure don sha'awa ba shakka zai fi ba kyawun ƙira mahimmanci sama da komai, wanda kuwa zai yi don soyayya shi kam kyawun hali ne gaba da komai, sha'awa in ta sami abin da take so ƙarewa take yi, soyayya kuwa ba ta farawa sai ta sami abin da take buƙata, wannan ya sa muke cewa ba wata soyayya kafin aure, don kashi uku na rukunnanta ba su hadu ba, sha'awa ce take dabaibaye manema da zarar an yi aure sati daya zuwa biyu, sai ka neme ta ka rasa, ta sami abin da take so ta yi gaba. To irin wannan nazarin shi ya sa nake ganin auren bazawara ya fi budurwa, in dai zancen soyayyar za a yi sosai, domin ita ta gama sanin namiji da sirrinsa, ta san me yake buƙata, kuma me za ta ba shi ya gamsu?

Ita kuwa budurwa haka wayam take zuwa, masamman 'yammatan cikin birni da boko ya cika musu ƙwaƙwalwa, suka dauki surutan ƙarya da suke karantawa a littafan Yammaci ko fima-fimansu a matsayin soyayya, suka fahimci cewa maigida shi ne zai yi wa uwargida hidima ita sai dai ta ci ta kwanta, wai wannan ma haka shari'ar muslunci ya gindaya, tsakani da Allah zawarawan da za su yi maka hidima sun fi su, kuma zamantakewa da su ta fi ƙarfi. To sai dai Annabi SAW ya kwadaitar sosai game da auren budurwa, masamman a wani hadisi da Tirmithiy ya ce Hassan ne kuma sahih, ya ce: Jabir bn Abdillah ya ce: "Na auri wata mata, sai na zo inda Annabi SAW, ya ce: Jabir ka yi aure ne? Na ce: Ƙwarai kuwa, manzon Allah. Ya ce: Budurwa ce ko bazawara? Na ce: A'a, bazawara ce. Ya ce : Da ba ka auri budurwa ba kana wasa da ita tana wasa da kai? Na ce: Na ce: Manzon Allah (Babana) Abdullah ya rasu ya bar 'ya'ya mata 9, sai na zo da wace za ta tarbiyantar da su, sai ya yi min addu'a.” . Akwai ma wata ruwayar ta Bukhari wace Annabi SAW ya ce: {ما لك وللعذاري ولُِعابها} Ba ga Ƴammata nan ba da wasa da ita! A nan in mun dauka cewa kasra ce a ƙasar Lam to ya ƙarfafa hadisin baya kenan na yin wasa da dai sauran abubuwan motsa sha'awa, don gudanar da sunnar manzon tsira, in kuwa mun dauka rufu'a ce a saman Lam din to kinaya ce na dan yawun da ake samu wurin sumbanta a yayin wasan, almuhim Annabi SAW ya nusar da shi ne abin da yake buƙata, kamar yadda kowani mai yin aure yake buƙata.

Ni kuma na ce kenan duk wani mai neman aure yana da matuƙar amfani ya tabbatar da cewa zai iya samun wannan wasan a wurin wace zai aura, don masu nazari sun gano cewa samun wasan yakan taimaka wajen zafafa jiki, da tafasa ruwan maniyyi gami da ƙara ƙarfin tunkudansa, kenan yana da tasiri har ga abin da za a haifa ba ma su mahaifan kadai ba, shi ya sa za ka ga wasu masu hangen nesan suna ƙyamar auren zumunta, sabo da wannan 'yan uwantakar wani lokaci takan hana samun abin da ake buƙata masamman ta ɓangaren matar, ita kuwa bazawara takan ga kamar ta girma wannan wasan ta bar wa yara.

Zawarawa dai a yau suna suka tara:- 1) Ga sakin wawa. 2) Ga kuma wace mutuwa ta yi awon gaba da mijinta tabar ta yarinya danya shataf masamman wannan lokacin ma na yaƙi, da cututtuka marasa kangado. 3) Ga kuma rashin sanin matsayin namiji ko na ita matar, wanda hakan shi ma yana haifar da sake-sake. A taƙaice dai duk macen da take son ta riƙe namiji tamtam lallai ta kula da gabansa sosai, in don tana ganin kamar cewa shi malami ne, ai ba wanda ya fi shi son sunnar Annabi SAW, ba wani kawaici ko girma a wannan harkar, shi ya sa tsahhin malaman ma suke auro yara don a yi wasan da za a sami lada da yawa. Ba shakka yarantar da irin wasan da ake yi suna ƙara wa namiji son auren budurwa, su ma matan sun san haka, shi ya sa za ka ji wata tana cewa " Ai na tsufa dole ya je wajen mai sabon jini wace za ta iya ba shi abin da yake nema! A'isha RA ta ce wa Annabi SAW: Da za ka shiga wata fadama wace akwai bishiyar da (dabbobi suka riga) suka ci, da kuma wace ba a ko taba ba, a wacce raƙumanka za su yi kiwo? (Sai Annabi SAW) ya ce "Wace ba a yi kiwo a kanta ba" tana nufin Annabi SAW bai auri budurwa ba ban da ita. (Bukhari) . A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  15)

Post a Comment

0 Comments