Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na 14)

Wannan na ɗaya daga cikin jerin rubuce-rubucen da Zauren Markazus Sunna ke samarwa kan batutuwa daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan karon rubutun ya shafi “Bambancin Sha’awa Da Soyayya” wanda Baban Manar Alƙasim ya rubuta.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  14)

Baban Manar Alƙasim

Abin da babu gardama a ciki shi ne: Allah cikin ikonsa ya daure tsakanin aure da sha'awar irin ta saduwa, bai bar abin a sake ta yanda sai an yi auren sannan a yi sha'awar mace ko ita ta yi sha'awar namiji ba, wata-ƙila da mutane -tsakanin maza da mata- an guji wannan Sunnah mai ƙarfin gaske, sai Allah SW ya sanya saduwar ta zama ginshiƙi mai ƙarfi ga rayuwar dan adam kamar cin abinci, barci da shaƙar numfashi, kenan dole mutum ya buƙaci saduwa, sai dai kuma in bai bi ta halas ba dole zai bi ta haram. A shari'ance aure ibada ne kuma neman kusanta ne ga Allah SW, domin in da mutum zai sadu da iyalinsa, duk da cewa su biyun buƙatunsu suka biya, har wata lada zai samu a wurin Allah SW matuƙar dai ya tsarkake aikinsa da kyakkyawar niyya, shi ya sa muke ba da shawarar cewa kar mutum ya fara neman aure kawai don sha'awar yarinyar da ya yi, wanda galibinmu kyawun jiki da fuska da iya ado da magana yake fisgar hankalimmu, mu yi kuma tunanin cewa ibada ne aure har ma saduwar, a wani hadisi na Muslim da na karanta na iske inda Annabi SAW yake cewa:

"Akwai sadaƙa a saduwar dayanku da iyalinsa" sai (sahabbai) suka ce: Ashe dayammu zai biya buƙatar sha'awarsa sannan kuma a ba shi lada a kai? (Annabi SAW) ya ce "A ganinku da a haram ya yi fa (wato fahasha kamar zina da auren holewa), shin akwai zunubi a kansa?" Suka ce: Ƙwarai kuwa. Ya ce " To haka kuma in ya saka a cikin halas (wato a aure na shari'a) yana da lada. Muslim, Abu Dawoud, Ahmad. A wani addini ne za ka sami irin wannan gatar? A hana kowa ya ji ƙamshin matarka, a hana shi ganin kwalliyarta ko wani sassa na jikinta bare ya tabi jikinta koda da musafahar gaisuwa ne sai dai kai kadai kawai? Sannan ka sadu da ita kamar yadda kowace dabba take saduwa da daya jinsin, amma kai taka saduwar ta zama ibadar da Allah SW zai ba ka lada a kai, ko ma na ce ta zama hanya ta neman kusantaka ga Allah SW kamar sauran nau'o'in ayyukan sadaƙa? Wannan shi ne muslumci, wanda yake daukaka saduwar namiji da mace abu mai daraja mai girma, ya mayar da abin da ake gani kamar al'ada ne ya koma ibada, wanda ake gani kamar hanyar rage sha'awa ce ta zama hanyar neman yardar Ubangiji.

Wato dai babban abin da ake buƙata wurinka kai mai neman aure, ko ita mai amincewa a aure ta shi ne: A sami tsarkakakkiyar niyya wace ya za ta kawar wa mutum da tunanin cewa zai nemi aure ne kamar yadda ya taso ya ga ana yi, ta sanya masa a zuciya cewa ya kai matsayin da zai fara wata ibadar ƙari a kan wace yake yi, bautar Allah kuwa ba a yin ta da saba masa, dole tunanin mutum ya zama kame ido, kunne, hanci da gaba daga saba wa Allah, ba wai kuma a yi aiki da sabon wajen neman aure ba.

Dole dai manufar ta zama buƙatuwar kamewa ne da nisantar holewa da diyoyin jama'a, da kuma cin ma manufar da Allah SW ya halicci mutum a dalilinsa, wato samun zuriya ta gari, wace in ba ta ba yadda za a yi adadin jama'a ya ci gaba da habaka har duniya ta sami jama'ar da za su zauna a cikinta, don haka da Allah SW ya hana saduwa da mata a ranakun azumi ya ce (To yanzu ku take su, ku nemi abin da Allah ya wajabta muku), wato ba manufar aure ne ba kawai a kawar da sha'awa, har da ƙaunar juna da hayayyafa yadda Annabi SAW zai yi alfahari da al'ummarsa ranar ƙiyama. A nan ne za ka ga son kan maza, yadda da zarar ta haska masa a ido ta liƙe 'yar muryarta gami da murmushi, ga ƙamshi da kwalliya, shi kenan ta gama da shi, ba ruwansa kuma da tunanin ko za ta iya riƙe masa 'ya'ya ko ba za ta iya ba, bare kuma ya yi tunanin dabi'unta da halayenta, abin da ya sa a gaba kawai shi ne, in dai ta shigo gidansa komai zai canja, don ba zai yarda da diban albarka ba, lamarin kuwa ba haka yake ba, mace in Allah ya mallaka maka ita, matuƙar za ka yi mu'amalla da ita kamar yadda muslunci ya tanadar, to tun farko ka nemi ta gari kawai, ba abin da ya fi ruwa taushi amma kisa yake. A nan zan dakata. Sai mun haɗu a rubutu na gaba.

Bambancin Sha'awa Da Soyayya (Kashi na  14)

Post a Comment

0 Comments