Yadda Aka Ɗora Mu A Keken-Ɓera

    Matakan samun sauyi da cigaba a rayuwa...

    Daukaka

    Hamza Dawaki

    Wasu birai ne guda uku, aka ajiye su a cikin wani dan daki. Suna zaune a ciki ba tare da sanin dalilin kawo su wurin ba. Sai daya ya kyalle idanunsa sama, sai kuwa ya hango tankar ayaba, nunannu lugub! 

    Ya tashi da sauri ya kama matattakala ya fara hawa sama, da niyyar daukowa. Bai ankara ba sai kawai ya ji an saita kansa da wata katuwar mesa (tiyo), an feso masa ruwa mai karfin gaske! Ya fado kasa tik! Ruwan nan kuma ya feshe har sauran biran nan biyu da ba su hau wurin ba.

    Daga baya sai aka dauke biri daya daga cikin na kasan. Aka bar wanda ya hau din da daya da bai hau ba. Aka kara sako wani sabon biri cikinsu. 

    Jim kadan sabon birin nan shi ma ya kyalla idanu ya hango ayabar can. Sai ya tashi da sauri da zummar hawa ya dauko. Ai sai kawai biyun can suka hadu suka kama shi, suka yi masa dukan tsiya! (Saboda suna tsoron kar ya janyo a kara feso musu ruwan.)

    Sai kuma aka kara dauke wanda ya fara hawan. Aka bar wanda ya san ana feso ruwan da wanda aka daka, ba tare da sanin dalili ba. Aka kara sako wani sabo. Shi ma ya ga ayaba, ya tashi zai dauko, biyun can suka kama shi suka yi masa lilis! 

    Sannu a hankali duk aka debe wadanda suka san ana feso ruwan da daidai. Amma fa duk da haka duk wanda aka sako, da ya tashi zai dauko, sai biyun su kama shi su yi ta jibga! Tare da cewa su ma ba su san dalili ba. Kawai dai sun ga duk wanda  ya yi yunkurin hawa haka ake yi masa! 

    Abin dariya ko? 😃

    To manta da su goggon birin, dawo da abin kaina da kanka. Yi tsai, ka duba yadda muke gudanar da lamuranmu na yau da kullum. Shin bai yi kama da wannan ba?

    Wasu ne suka juyar da tunaninmu cewa:

    * In ba boko ka yi ba, ba za ka samu aiki ba!

    * In ba ka tanadi jari ba, ba za ka taba zama dan kasuwa ba!

    * In kai dan talaka ne, ba za ka yi arziki ba!

    * In ba a babbar jam'iyya kake ba, ba za ka taba cin zabe ba!

    * In kai ba Bature ba ne, ba za ka taba kirkirar mota ba!

    * In kai.. 

    * In.

    Ina ganin lokaci ya yi da ya kamata mu FARKA.

    Daga falsafar: #AGAJE-NI-MU-GYARA👌

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.