Ya Saki Matãrsa Cikin Rashin Lafiya Da Ya Rasu A cikinta, Shin Matar Zata Ci Gadonsa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Miji ne ya saki matarsa alhalin yana cikin rashin lafiyar da ya rasu a cikinta, shin matar da a ka saki ɗin za ta iya cin gadonsa ko a'a?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dukkan Mālamai sun yi ittifaƙi a kan cewa idan maras lafiya ya saki matarsa to sakin ya yiwu, kuma idan ya mutu a cikin wannan rashin lafiyar kafin matar ta gama idda to za ta ci gadonsa kamar yadda ko da lafiyarsa ƙalau ya saketa kuma daga ba ya sai ya mutu kafin matar ta gama idda to za ta ci gadonsa. Hakanan Mālamai sun yi ittifaƙi a kan cewa idan mutum yana cikin rashin lafiyar mutuwarsa sai ya saki matarsa kuma sai ita matar ta rigaye shi mutuwa, to mijin ba zai ci gadonta ba ko da kuwa ta mutu ne kafin ta gama idda.

    Sai dai Mālamai sun yi saɓani game da maras lafiyan da ya saki matarsa saki uku kuma sai ya mutu kafin ta gama idda, shin itama za ta ci gadonsa ko ba za ta ci ba?

    Mafi yawan Mālaman da ke Mazhabobin Hanābila, Mālikiyya, da kuma Hanafiyya.

    Sun tafi ne a kan cewa za ta gaje shi ne sakamakon tuhumarsa da a ke yi a kan cewa dama ya saketa ne don ya haramta mata cin gadonsa, danhaka sai Mālamai fuƙaha'u sukayi amfani da wasu āsār da a ka samu a wajen magabata, da kuma ka'idar nan ta fiƙihiyya da ke cewa.

    "من تعجل الشيء قبل أوانه عوقب بحرمانه"

    MA'ANA

    Wanda ya gaggauto da wani abu kafin lokacinsa ya yi sai a yi masa uƙuba ta hanyar haramta masa wannan abin.

    Kamar misālin Mutumin da ya kashe mahaifinsa don yaci gadonsa, sai shari'a ta haramta masa yaci gado, to tunda shima wannan mijin a na tuhumar ya saketa ne saboda ya haramta mata cin gadonsa danhaka idan har yamutu a cikin wannan rashin lafiyar to matar za ta gaje shi, hakanan kuma inda mutum zai kamu da rashin lafiyar da a ke ganin mawuyaci ne ya tashi a cikinta, to shima inda zai auri wata mace a lokacin kuma sai ya mutu a cikin wannan rashin lafiyar to itama ba za ta gajeshi ba, domin a na tuhumarsa ne a kan cewa yana so ne itama wannan matar ya janyo ta tashigo cikin sahun masu cin gadonsa shiyasa ya aureta a lokacin.

    Amma a wani kauli na Mazhabin Shāfi'iyya da Zāhiriyya sun tafi ne a kan cewa ita matar da a ka yiwa saki uku ba za ta gajeshi ba ko da kuwa ya mutu ne kafin ta gama idda, domin ya yi mata saki ne manisanci irin wanda ba a yin kome a cikinsa.

    Danhaka a nan sai Mālamai sukayi saɓani dangane da cewa shin a wanne lokaci ne matar ta ke da haƙƙin ta ci gadonsa? Mazhabin Hanafiyya sukace matar da a ka yiwa saki uku sai mijin ya mutu kafin ta gama idda to za ta ci gadonsa, amma idan sai da bayan ta gama idda ne sannan ya mutu sukace ba za ta ci gadonsaba

    Su kuma Mazhabin Hanābila sukace za ta iya cin gadonsa ko da bayan ta gama idda ne amma da sharaɗin kafin ta yi aure, sukace indai har ta yi aure to ba za ta gajeshi ba, domin ta saryar da haƙƙinta na cin gado da wannan aure, sai dai Mazhabin Mālikiyya sun tafi ne a kan cewa ai ko da ta gama idda harma ta yi aure to za ta iya cin gadonsa, saboda waccan ka'idar ta fiƙihiyya, sukace domin za ta ci gadonsa ne bawai dan saboda alaƙar auratayyarsu ba, sai dai za ta ci gado ne sakamakon waccan illar da tasa mijin ya saketa don kar taci gadonsa.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

     Mυѕтαρнα Uѕмαи

     08032531505

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.