𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Dan Allah Ina san Ƙarin Bayani
Akan Wannan Hadisin, { Ban Bar Wata Fitina Abayana Ba Wacce Tafi Cutar Da Maza
Kamar Fitinar Mata Ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله العزيز المنان.
Wannan hadisin shi ne hadisin
Usama bin Zaid Allah yaƙara yarda dasu wanda Bukhari (5096) da Muslim (2740)
Suka ruwaitoshi.
Saboda Mace ita ce abar kallan
Maza, Allah ya dorawa namiji ya halittaceshi akai ya sanya masa sha'awar
karkata zuwa ga mace, yaso ko baiso ba, wannan al'amarine da'aka halicci namiji
a kansa, mace ita ce abar jin daɗin namiji, idan ya kalleta jijiyoyin kai saƙo
zuciyarsa za su motsa, saboda haka shari'a ta Umarceshi ya runtse ganinsa,
Zuƙata suna shaƙuwa da leƙawa
zuwa sha'awar mace, Allah ya sanyawa matune sha'awowi kamar yanda ya ce:
ﺯُﻳِّﻦَ ﻟِﻠﻨَّﺎﺱِ ﺣُﺐُّ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ
ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨِّﺴَﺎﺀ ﻭَﺍﻟْﺒَﻨِﻴﻦَ ﻭَﺍﻟْﻘَﻨَﺎﻃِﻴﺮِ ﺍﻟْﻤُﻘَﻨﻄَﺮَﺓِ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺬَّﻫَﺐِ ﻭَﺍﻟْﻔِﻀَّﺔِ
ﻭَﺍﻟْﺨَﻴْﻞِ ﺍﻟْﻤُﺴَﻮَّﻣَﺔِ ﻭَﺍﻷَﻧْﻌَﺎﻡِ ﻭَﺍﻟْﺤَﺮْﺙِ .{ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ 14 }
Mun ƙawatawa mutane son Ababen
sha'awa daka mata da 'ya'ya da kayan ƙyale ƙyale na dinare da Azurfa.
'ya'ya suna zuwa daka mata, hakan
kuma baya samuwa saida jima'i, mata sune mafi girman fitina saboda haka Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Duniya Abace mai zaƙi mai kwarran shukoki
ababen ƙaye wajan kallo, Allah ya sanyaku a cikinta yaga yaya zakuyi aiki, kuji
tsoran duniya kuji tsoran mata, domin farkon fitinar data samu Banu isra'ila
tasame sune ta hanyar mata.
Muslim (2742).
Haduwar mata da maza da
chakuduwarsu awajan aiki ko kasuwa fitinace mai girma, saboda Annabi sallallahu
Alaihi wasallam ya ce: Mace idan ta fuskanto namiji tana fuskantoshi ne asifar
Shaiɗan, haka idan ta juya masa baya.
Turmuzi (1158) da ibnu hibban a
cikin Sahihin littafinsa (5572) Albani ya ingantashi a cikin sahihul
jami'issageer (845)
Shi ya sa zakaga duk inda namiji
yake Hankalinsa ya kan mace, akan hanyane a kasuwane awajan aikine da sauran
gurare, ko akafafen internet zakaga inda hoton mace anfi rububin zuwa wajan
campanoni Sunfi amfani da hotunan mata, kai hatta mutumin dayake hatsabibi
akesan shammatarsa sai abi kowacce hanya yagagara amma da Anbi ta hanyar mace
cikin ƙan-ƙanin lokaci za'aci nasara a kansa.
Haka idan mutum jarumine tsayayye
idan baiyi taka tsan-tsan ba sai kaga anyi amfani da mace an rusa shi.
Koda ƙasashen musulunci da
musulamai da'akasan akwai sauran ruhin musulunci atare dasu kuma shugabanninsu
suna da Addini gwar-gwadon hali, ba'aci nasara a kansu ba saida akabi tahanyar mata
tsala-tsala aka aura musu.
Shi ya sa Namiji idan yai Aure baya
kubuta daka halaye guda uku.
Wani bayan ya yi aure yake samun
kansa cikin tasku da kidimewa, macen dazata rikita masa hankalinsa tazo,
Musamman idan kyakkyawace bata tsoran Allah, ba zai iya ƙin yi mata duk Abun da
ta nema ba, shiyasa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Ban taɓa ganin
mai tauyayyen hankalin da yake tafiya da hankalin namiji jajirtacce kamar mace
ba.
Bukhari (1462) da Muslim (79).
Wanda yake wanzuwa ahalin da yake
kafin Aure, Amma kaɗan ne idan yasamu mace mai tsoran Allah, saliha mutuniyar
kirki.
Inko bai samu wannan ba, zata
dunga shagaltar dashi ne, yau daukeni muje rastuarant kaza, yau muje gidan zoo,
gobe muje super market, jibi mutafi wajan shaƙatawa, zata shagaltar dashi daka
komai sai hutun kanta dajin dadinta, wannan fitinace.
Shiyasa Allah Madaukakin Sarki ya
ce:
إِﻥَّ ﻣِﻦْ ﺃَﺯْﻭَﺍﺟِﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻭْﻟَﺎﺩِﻛُﻢْ
ﻋَﺪُﻭًّﺍ ﻟَّﻜُﻢْ ﻓَﺎﺣْﺬَﺭُﻭﻫُﻢْ {ﺍﻟﺘﻐﺎﺑﻦ 14.}
Lallai A cikin matayenku da
'ya'yanku akwai waɗanda fitinace ku kiyayesu.
Ibnu Ƙayyeem ya ce: Wannan adawar
bata ƙiyayya dajin haushi bace, ƙiyayyace wacce tushenta shi ne so da tausayi,
idan zakai sallah tace kazauna taganka kadauke mata kewa, idan zaka fita tace
in kafita hankalinta tashi yake tsoro takeji, idan zaka neman ilmi tace ina
zakaje, zaka barni nikadai a gida ina shiga ƙunci, idan zai umara ta hanashi
idan zai aikin hajji tahana, idan zai kyautatawa 'yan'uwansa ta hana, duk wani
aikin alkhairi idan zai yi sai ta hanashi, aƙarshe sai kaga wannan ƙiyayyar
tazama kamar ƙiyayyar bakin ciki dajin haushi. Sai Mutum yawayi gari yanada ƙarancin
ayyukan alkhairi, duk saboda mace ko dah.
Amma Allah baice dukkan Mata ko
'ya'ya ba, wasu daka cikin mata da 'ya'ya ba haka sukeba, daka cikin mata akwai
wacce ita ce take gyara namiji, ita ce take umartarsa da ayyukan Alkhairi tana
hanashi aikata mummuna, wani lokacin yanaƙi wani kuma ya Amsa, ba dukkan mata ko
'yaya ne suke zama fitina ba.
Namiji idan ya zauna agaban mace
kamar yanda ibnu hazam ya ce: jikinsa zai fara motsi kamar kafadarsa da kansa,
da idansa ba tare da sonsa ba, saɓanin idan agaban maza yazauna, wannan Abune
sananne.
Wannan fidrace Babu mai ja a
kanta sai Namiji mai girman kai,
Waɗannan Ababe Sune Abun da
wannan hadisi yake nufi, (Ban bar wata fitina abayana ba, wacce tafi cutar da
maza sama da fitinar mata).
WALLAHU A'ALAM.
Tambaya da Amsa Abisa fahimtar
magabata Nakwarai.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.