Ticker

6/recent/ticker-posts

ADADIN KWANAKIN JININ HAILA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Nawa ne Ka'idar yawan kwanakin jinin haila sannan kwana nawa yake ya kare?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ 

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ 

Da farko: Idan haila tazo ma mace, to lokacinta na karewa ne idan jini ya dauke. Ba tareda la'akari da jinin dan kaɗan bane ko mai yawa ne.

Mafi yawan malamai sun ce mafi Karancin kwanakin al'adar mace shi ne Wuni ɗaya da dare ɗaya (1day and 1 night). Sannan mafi tsawon lokaci shi ne Kwanaki goma sha biyar (15days).

Shaykhul Islam Ibn Taymiyyah (Rahimahullah) ya ce: babu karancin adadin Kwanankin haila, haka kuma babu adadin tsawon kwanakinta. Idan jini ya fito da kamannun haila, to wannan jinin Haila ne, koda kaɗan ne ko mai yawa ne. Ya ce;

Allah ya alaaƙanta Haila da hukunce-hukunce masu yawa acikin Alƙur'ani da Sunnah. Amma bai ambaci adadin karancin kwanakin ta ko mafi yawan kwanakin ta ba, ko tsawon lokacin tsarki tsakanin wata Haila zuwa wata Haila. Duk da yake akwai bukatar sanin haka.

Sannan ya ce: Wasu malamai sun ambaci karanci da mafi tsawon kwanakin ta, amma sun bambanta a hakan.

Wasu malami kuma sun ambata adadin mafi tsawon kwanankinta amma basu ambaci karancin kwanankinta ba.

Ra'ayi Na uku wanda shi ne yafi zama daidai shi ne Haila batada karancin kwananki kuma batada adadin yawan Kwanankin daukewarta.

(Majmu'ul Fataawaa, 19/237).

والله أعلم


Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments