Waɗan nan cututtukan na: Cancer, Ƙoda, Strock, Depression, Anxiety, hawan jini, Diabetics, Yawan mantuwa, Waswasi, Yawaita tsoro mara dalili, Matsalar ƙwaƙwalwa ko hauka, da kuma sauran cututtukan makamantansu za kaga SIHIRI yana shiga cikinsu tayadda za ayita maganin asibiti amma arasa fahimtar inda cutar ta fuskanta, duk wasu gwaje-gwajen da akeyi sai kaga suna bayar da sabanin abin da ake so agani.
SIHIRI yana iya sabbaba jinkirin Aure ko rashin auruwa da rashin haihuwa, yawan samun miscarriage ( barin ciki) akai-akai, Low ko week sperm count, ko rashin Ovulation ga mace ko matsalar Hormonal imbalance.
SIHIRI yakan iya shiga tsakanin mutum da dukiyarsa tayadda zai tayin almubazzaranci sai kaga ya rasa inda dukiyar ke tafiya nan da nan dukiyar ta kare ba tare da ya yi wani muhimmin abu da ita ba.
SIHIRI yakan iya shiga tsakanin ma'aurata har yaraba su, yaraba tsakanin Iyaye da ‘ya’yansu, ya raba tsakanin mutum da yan uwansa, ya raba tsakanin mutum da sauran mutane ko da kasuwancinsa, da dai sauransu....
SIHIRI yana matukar yin tasiri ne a jiki da kuma ƙwaƙwalwa shiyasa yake zama sababi na wasu cututtukan kuma kaga mutum yayita aikata wasu ayyukan ba tare da ya san yana aikatawa ba akarshe kuma sai nadama ta biyo baya.
"AMMA DUK WANNAN BA SU DA IKO KO DAMAR TABBATAR DA CUTARSU GA KOWA DOLE SAI DA IZININ ALLAH"
A dage da karatun Alƙur'ani da sauraronsa da yin Azkaar a ko da yaushe sai riko da ingantattun sabubban da basu sabawa Addinin Islama ba.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani
sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar
da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba
maganin ba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar AlÆ™asim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.