KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 32

    5) KALLON WASU: Wannan ma na daya daga cikin abubuwan dake kawo kishi a matattararmu, wato lokacin da mace ta kalli yadda mijin wata yake tattalinta amma ita nata kamar ma bai san Allah ya yi ruwan tsirarta ba, sai ta ga ana tarairayar wancan suna wasa suna dararraku in abin ya yi tsawo sai kishi ya shiga tsakaninsu duk da cewa ba miji daya suke aure ba. Wannan ya fi faruwa a gidan hadaka kamar gidan haya. Idan mace ta lura da cewa maÆ™ociyarta na cikin jin dadi. To ita me ta rasa? Me zai sa ba za a yi mata irin  abin da ake yi wa wancan ba? Me wancan din take da shi da ita ba ta da shi da za a riÆ™a yi mata ita kadai? Dalilin kishin kenan.

    Da farko akan kalle wannan ne kamar hassada, domin ba ta son ganin maÆ™ociyar a yadda take, sai in an duba da kyau a ga cewa mummunan kishi ne ba hassada ba.  abin da ya sa suka yi kama shi ne nuna rashi gamsuwa da jin dadin da wancan matar take yi da maigidanta, sai dai inda suka dan bambanta ba rasawar matar ce matsalarta ba, ita me ya sa ba ta samu ba? Ai ta fi wancan cancanta! Son kai ya shigo ciki, wanda shi ne Æ™ashin bayan mummunan kishi, sai an yi da gaske kafin a raba shi da hassada.

    In an lura tana matuƙar ƙaunar mijin wancan ba ne, ƙila ma haushi yake ba ta in ta gan su cikin fara'a da walwala, ita kuwa ga ta cikin kadaici da damuwa, ko wancan na samun komai ita kuwa wayam. Galibi irin wannan kishin kan kama mata da yawa in suna kallon fima-fiman Hausa ko na Indiya, don sukan riƙa ganin yadda wani ke kula da matarsa sosai su kuwa na su mazan ko goro bai kai fuskarsu shan dauri ba. Ba sai an yi dogon lissafi ba, mazansu ba sa kyautata musu, ba su iya soyayya ba, da sauransu. Amma me ita wancan matar take yi da har ta iya mallakar mijin da lokacinsa da komai haka?

    Abinda matammu ba sa bincikawa kenan, ba su san mace na da rawar da take takawa a wannan bangaren ba, ganinta kawai mijin ke komai. Shi ma ya kamata a ladabtar da shi, in suna amfani da makewayi daya ne to za ta yi ƙoƙari ta san lokacin da yake zagawa wanka, in ta shiga ba za ta fito ba sai ta tabbatar ya makara. Ba don shi za ta yi haka ba don ta baƙanta wa matarsa ne ta tabbatar ranta zai baci, to bare kuma a ce matar ta ƙwanƙwasa ƙofar masan! Zamanta za ta yi sai yadda hali ya yi.

    Wata akan kasa gane babban dalilin da ya sa take fada da maÆ™wabciyarta, ba wani abu ne babban dalili ba kishi take da su, ita a mijin, ta yadda yake matarsa komai ita nata mijin bai ko kwatantawa. In ta saka matar a gaba a wayar shanya ma sai an ji tsakaninsu, haka wajen sharar tsakar gida. A kullum za ka iske ana Æ™oÆ™arin raba su fada ba tare da dalili mai Æ™arfi ba. Ƙila ka ji wancan tana cewa "Ni wallahi ban san me na yi wa wance ba, duk ta tsane ni!"  abin da suke cewa ya kawo fadan ba shi ne dalilin ba kishi ne.

    Sau daya na sami labarin wata mata da ta auri mijin maÆ™wabciyarta. Ita ma ta Æ™yalla ido ne ta ga  abin da mijin maÆ™ociyar yake mata, duk kyautatawar da yake mata ba ta da lokacinsa bare na yaran tana wurin aiki, nan fa daya matar ta samo wata sana'ar sayar da kayan mata ta fara shigarsu a hankali har ta samo hankalin wancan, shedan ya sanya musu albarka duk suka rabu da abikan zamansu suka hade.

    Sau tari nakan ji ana magana kan alaÆ™ar so da kishi, wani lokaci akan ajiye su a wuri guda, wani lokacin a raba. Anan kam an dan sami kamancece niya, sai dai  abin da ya fi faruwa a tsakanin Hausa/Fulani in har matar wani na kishi da wasu to su biyun za ta yi tsama da su, don me matar za ta zama zabiyar mata ita kadai? Don me mijin yake zaÆ™ewa a kan wata ita kadai? ke nan ba Æ™aunar mijin wancan take ba, shi ma din tana jin haushinsa, da ya fara nuna wa matarsa kulawa ranta zai baci. Amma da zai fara cutar da ita zuwa nan gaba ba za ta so ba, sai dai za ta ce haka maza suke don nata ma haka yake.

    Wannan nau'i na kishi a kan mijin wata ba baÆ™on abu ba ne, duk wacen da ta zauna a gidan haya ba za ta rasa  abin da za ta fada ba sai dai in tana kebe ne ba ta san  abin da ke kaiwa da komowa a wani wurin ba. Akan wannan kishi wasu matan kan maÆ™e suna sauraron  abin da ke faruwa a maÆ™wabta. Wata za ka ji ta kawo yadda harkar shimfida ke wakana a maÆ™wabta har ka yi tsammanin gulma ce kawai ko yawan surutu, a zahiri kishi ne ya kawo haka.

    Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u a Rubutu Na Gaba.

    **************************
    Daga:  Baban Manar AlÆ™asim
    **************************

    Wannan É—aya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faÉ—akarwa da ilimantarwa, waÉ—anda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun Æ™arin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waÉ—annan rubuce-rubuce, amma tana É—ora su ne da izinin Baban Manar AlÆ™asim.

    Kishi Rahama Ne Ko Azaba

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.