Ticker

6/recent/ticker-posts

KISHI RAHAMA NE KO AZABA // 30

 ME ZA SU YI SU HANA KISHIYA?

Matar dan ƙwalloncan da muka karanta a baya da wahala ta sami matsala da maigidanta, ta san shi sosai, gasunan sun tsufa amma ita kadai ce ƙwallin-ƙwal a cikin gidansa, baida buƙatar ƙaro wata matar, daga ita sai yaranta sai kuma 'yan aiki. Tabbas tana da mugun kishi, duk da haka ta san yadda za ta seta maigidanta, a ƙarshe dai kishiya ce ba ta so. Kuma ta hana ta shigowa ba tare da ta baƙanta wa kowa ba.

Na fi gasgata irin wadannan matan sama da wace za ta ce ta yarda da mijinta dari bisa dari ta san ba zai taba kallon mace da wani ido ba, amma ba  abin da ta yi a ƙasa wanda zai tabbatar da hakan. Duk wace ta yarda maigidanta ba zai taba yi mata kishiya ba, sai ta ji an ce yana zuwa wurin wata, ita ce ke cewa mutuncinsa ya zube gaba daya a idonta, ba ta taba tsammanin zai yi mata ƙarya ba, ashe maƙaryacin gaske ne, nan take za ta ce ya ci amanarta, bayan ta dauki duk yardarta ta ba shi.

Wata ma ƙila tana da kudin gado an raba an ba ta nata ta dauko ta danƙa masa don ya ja jari su zauna cikin aminci ita da 'ya'yanta, a dalilin haka sai ya yi arziƙi da dukiyar babanta, bayan ya sami  abin da yake so, ta bakinsu, sai ya ci amanarta ya dauko mata wata. Ku ce ta duba kanta a ina aka sami matsalar? Galibi matsalolin da ake samu wadanda suke kai namiji ga ƙara aure kashi 70 cikin dari matan ke jawowa. Kodai matarsa kai tsaye, ko uwarmiji, ko wata ta fada cikin idonsa.

Amma matan gida ku lura da kyau wata ƙyuya ce da ita, wata son jiki, wata girman kai, wata masifa a cikin gida, wata rashin girmamawa, wata rashin zama a gida, wata ba ta gyara shimfida yadda ya kamata, wata ba ruwanta da 'yan uwansa ko uwayensa, wata ba ta da lokacinsa duk  abin da ta rasa akwai wace za ta rufe wannan mahallin. Da yawan mata sai an yi musu kishiya suke fara tunanin yadda za su lallaba mazan, alhali ya dace ne a ce sun yi tun kafin mutum ya fara tunanin shigowa da wata.

Akwai macen da ta ce min ita fa in namiji ya yi mata ƙarya sau daya tal wallahi ya gama sure mata gaba daya, ba za ta kuma yarda da shi ba har abada, na kalli na kusa da ni muka tuntsure da dariya, don  abin da ya gaya mata a ranar ba wanda yake gaskiya, ban sani ba ko akwai mazan da ba sa yi wa masoyansu ko matansu ƙarya, amma lokacin da nake zuwa karatu wani wuri na taba jin malaminmu yana cewa akwai kalar ƙaryar da shari'a kan daga mata ƙafa, ya lissafo kusan uku, a ciki har da wace miji zai yi wa matarsa don neman zaman lafiya.

Muna maganar kishi ne a matattararmu, da yadda ake yinsa da kuma yadda ya kamata a yi. A gaskiya matan Hausa fulani na da ƙoƙari amma ta wasu bangarorin. Misali ya kamata a ce malami in ya tashi aure ya auro dalibar ilimi irinsa wace ita ma karatun ne a gabanta, abin takaici da yawanmu hanyar da gama-gari kan bi ta wurin zaben abokiyar zama mu ma ita muke bi, to in muka auro ta sai ka ga ba karatun ne a gabanta ba, ga shi karatun miji da mata bai cika dorewa ba, shi yana mata kallon dalibarsa a lokacin da yake son koyar da ita, ita kuma tana yi masa kallon maigida.

Sai ka ga ya yi fushi a ƙarshe karatun ya ƙi yuwuwa, da a dalibar ilimi ya auro ba matsala, ko bai sauko da littafai ba da kanta za ta ciro ta karanta ta mayar, in shi ya ciro ta san inda za ta saka. Wace ba ta da alaƙa da ilimi kuwa gani take yi kamar dora mata aiki yake yi, kullum ya ciro littafai sai ya bar mata a ko'ina. Irin abubuwan da take masa na ma'amalla a cikin gida sai ya ji a lokacin yana da buƙatar ƙaro wata matar wace za ta iya yi masa  abin da yake so, da matar ta jure ta da shi kenan. To yanzu in ta fara kishinta sai ka ji ana cewa kamar ba matar malam ba.

Matan malamai har kishi suke yi da dalibansa, wani malamin fa sai ya hada makwanni biyu bai je wajen wata ba, matan akan raba su ne a jahohi, to in ba a yi dace ba sai ka ga malami ya auro wata mai kudi da ta ga shuhurarsa, karatunsa ya burge ta, in fa ta aure shi ba wahayi za a yi mata ba, karatun dai babu, yau ta yi salfi da shi ta dora a kafar sadarwa don nuna wa sauran matan, gobe ta ja shi su je bakin ruwa don shaƙatawa. Ita kuma da haka take kishinta wasu lokutan ganga kan yi zaƙi da yawa har ta fashe, in ba a yi sa'a ba kuma kishin uwargidan ya taso ta ba ta auren.

Ba malamai kawai ba akwai 'yan kasuwa da manyan ma'aikatan gwamnati masu yawo daga wuri zuwa wuri, su ma sukan kasa aiwatar da wasu abubuwan na cikin gida kamar yadda ya dace ciki harda shimfida. Nan ne za ka ga matan sun fara kishi da cewa mazan na neme-neme a waje, in ba a yi sa'a ba su ma su dauki mataki irin haka, ko kuma, su fara zargin cewa ai ya fi son wata shi ya sa kullum yake zuwa wurinta, ba ruwansu da zarafin aiki da yadda ya juya. Kafin a shawo kansu da wahala, wata ma da haka za ta sarayar da auren.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments