SHIN YA HALATTA NA ROKI ALLAH YA KARAMIN WATA ABU DAKA CIKIN HALITTAR DA YAYIMIN?

      

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam dan allah inada tambaya shin akwai laifi idan naroki allah yakaramin wani abu daga cikin irin halintar dayaimin nagode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalamu Warahmatullah.

    'Yar uwa, ya na daga cikin ladubban yin addu'a, wato yin Koyi da Biyayya ga Annabi (ﷺ) a lokacin addu'a. Domin Allah (ﷻ) Yana cewa:

    وَاتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُم تَهتَدُونَ

    MA'ANA: “Ku bi shi, mai yiyuwa kun samu shiriya” (Al-a'raf 158)

    Saidai kuma, a gaskiya ni ban san wani nassi da ya zo cewa Manzon Allah (ﷺ), ko sahabbansa, ko wasu magabata na Kwarai na rokon Allah a kan ya kara masu wani abu daga surar jikinsu ba.

    Sannan, malamai suka ce, yana daga cikin sharuddan addu'a; kada mutum ya roki abin da a al'adance ba mai yiwuwa bane, ko ya Saɓawa dabi'a, Wanda kuma hakika tambayarki ta yi dai-dai da wannan ƙaulin.

    Duk wata halitta da Allahu (SWT) Ya yi, to akwai hikima a cikin hakan, ba wai don Allah ba ya son mutum bane yake yo shi gajera, ko dogo, baki ko mummuna, A'a, Shi Allah Ya na halitta ne yanda yake so ba yanda mutum ya so ba. Allah (ﷻ) Yã ce:

    وَرَبُّكَ يَخلُقُ مَا يَشَآءُ وَيَختَارُ مَا كَانَ لَهُمُ الخِيَرَةُ....“

    MA'ANA: “Kuma Ubangijinka Ya na halittar abin da yake so ne kuma ya zaɓa, zaɓi bai kasance a gare su ba....” (Al-Ƙasas: 68)

    Don haka, a gaskiya a tamu fahimtar, bai halatta ki roki Allah Ya kara maki wata halittar jikinki wadda a al'adance ba bu wani tangarda a ciki, kamar ki ce Ya kara maki Kyau, Tsawo, Dogon hanci, ko wani abu makamancin hakan, wannan bai halatta ba.

    Amma idan wani abu ne wanda ya saɓawa al'ada, wanda har ya kai ga za a iya kiransa da lalura, to wannan babu laifi ki roki Allah Ya kawo maki sassauci in shaa'a Allah.

    Wannan shi ne abin da na sani, Allah ne mafi sani.

    🏿Ayyoub Mouser Giwa.

    08166650256.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.