MAGANIN ƘANƘANCEWAR NONO

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam dan Allah tmbyata anan ita ce shin meke janyo kankancewar nonuwa ajikin mace, kuma dan Allah idan akwai  abin da za'iya yi dan mangancewa faruwar haka toh malam dan Allah ataimaka min dan na rasa yadda zanyi. Nagode. Kuma dan Allah malam a ɓoye sunana.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dalilan da suke kawowa Ƙankancewar nonuwa ajikin mace, suna da yawa. Amma mafiya faruwa daga ciki sune:

    1. Jinya mai tsanani (musamman adaidai lokutan farkon balaga).

    2. Gadon dangi: idan ya kasance yawancin matayen danginki kamar mahaifiyarki, kakarki, ko Goggonki suna da irin wannan yanayin, to kema hakan zai iya shafarki.

    3. Yawan amfani da Kwayoyin rage Ƙiba. Ko kuma magunguna ba bisa Ƙa'ida ba.

    4. Sirantaka: Idan ke siririya ce sosai, to nonuwanki zasu iya zama Ƙanana. Domin kuwa Kitse ne yake taruwa aduk guraren bambancin halitta tsakanin Mata da maza. Kamar nonuwa, mazaunai, kutiri, etc.

    5. Adaidai lokacin balaga, Akwai wasu sinadari na kwayoyin halitta wadanda jikin mutum yake fitarwa. Wani lokacin kuma, ana samun matsalar ne idan jikin mace ya kasa fitar da isassun hormones ɗin da zasu gabatar da wannan aikin.

    MAGANI:

    1. Ki samu garin Hulba ta asali marar gauraye. Ki rika zuba cokali 2 acikin kofi guda na madarar shanu. Ki gauraya ki shanye kullum.... Tare da zuma. Amma fa ba madarar kanti ba. Sabuwar madarar shanu nace.. Idan baki samu ba, ko nonon akuyarki ko Tinkiyarki ki tatsa kiyi dashi.

    2. Ki samu man hulba original (made in egypt ko Saudia ko Syria) sannan ki samu man aloevera ki rika shafawa a nonuwan naki. In Shã Allahu zakiyi mamaki sosai.

    3. Ki yawaita cin kitse acikin abincinki (musamman ma Vegetable fat).

    Allah ta'ala yasa mudace

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.