Ticker

6/recent/ticker-posts

SHIN MACE ZA TA IYA SANYA TURARE TA FITA?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam

Mace na da turare sai ta sanya ta fita menene matsayinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ba duka sanya turare a jikinta yake zama haramun ba. Idan mace zata fita a gidan mijnta, yazama za ta ci karo da wasu mazan da ba nata ba (muharramai), to anan yana iya haramtuwa, saboda Annabi tsira da aminci su tabbata a gareshi ya ce "idan mace ta sanya turare bakur mai kanshi (irin wanda suke sawa a lokacin), Annabi ya ce koda Sallar isha Kar tazo ta yi damu"

Muslim 0444.

Meye dalili? Saboda masallacin ai akwai maza, to wannan babin ne malamai su kace Yakai matsayin haramun. Allah Ta'ala Ya haramta.

Akwai Hadisi Sahihul Tirmidhi 0142 da ke bayyana cewa laifinta ma yana iya kai matsayin zina in ta sanya turare taje wajen maza su ringa jin kanshin...

Akwai Hadisi da yazo a cikin Abu Dawud Hadisi na 1820 da yake bayyana cewa an samu a zamanin Fiyayyen Halitta mata sukan sa turare Mara karfi kamar a lokacin da suka yi wankan Ihrami yadda Shari'a ta amince, sai su dan saka a jikinsu haka, kamar wajen hammata, tsakanin cinyoyi saboda maganin kada Zafi yai yawa na tafiya jikin mutum ya dinga hamami, in suka yi wankan Ihrami sai su saka, sai su dora Kaya akai. Da wannan malamai ke ganin idan mace ta sanya turare Mara karfi a jikin kayanta sai ta samu hijabi yalwatacce da ba turare, ta rufe jikin dashi, ta sa a jikin ne dan ita ka da taji hamami in zufa (gumi) ya taru a jikinta, anan su kace babu laifi dan matan sahabbai sun saka sun rufe. Amma da sharadi yazama kanshin wanda ke wulgawa bazai ji ba.

In kuwa zataje ta zauna gaban Namiji ne, ko likita zai dubata, ko wani wurin da ake haduwa da maza, a magana mafi inganci na Ahlul-ilmi sanya turare a wannan hali yana kaiwa matsayin haramun.

An tambayi Sheikh Bin Bas (RH) a cikin fatawa tashi juz'i na 10 shafi na 40. Cewa menene matsayin idan Mace ta sa turare ta fita a gidan mijinta zataje wani taro, amma daga fita a gidan mijin maybe shi zai kaita a har ta dawo da mata kawai take haduwa babu Namiji, duka komai na mata, amma mijin ko danta zai kaita a Mota sai ta fesa turare, amma inda taje mata ne zallah. Meye matsayin wannan?

Sai ya ce in ya tabbata mata ne Kaɗai a wajen Halal ne ta saka.

Saboda illa din shi ne kada Namiji yaji taja hankalinsa, dan matuka da gaske turare yana jan hankalin mutum...

Mata inda akafi so su sanya turare shi ne a gidajen mazansu. Wannan shi ne a inda akeso mace ta nuna isa da iya gaye da kure adaka ta sa turare shi ne a gidan mijnta.

WALLAHU TA'AALA A'ALAM

Amsawa: Prof. Isa Ali Pantami

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments