𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikumus. da fatan Malam yana lafiya,.shin Shaiɗan yana cikin jinsin aljanu ne Ko Mala'iku kuma Dame Allah ya halacci mala'iku?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaykumussalam, to ɗan'uwa malaman tafsiri sun yi saɓani game da haka zuwa maganganu guda biyu:
1. Shaiɗan yana daga cikin mala'iku, saboda faɗin Allah a cikin suratul Bakara aya ta: 34, "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa da ya yi girman kai" toface Iblisa daga cikin waɗanda ba su yi sujjada ba, yana nuna cewa yana daga cikin mala'iku.
2. Shaiɗan Aljani ne, saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki "Kuma ka ambata lokacin da muka ce da mala'iku su yiwa Annabi Adam (A.S) sujjada, sai suka yi sujjada, in ban da Iblisa, wanda ya kasance daga cikin Aljanu ("Kahaf aya ta: 50) sai ayar ta bayyana cewa daga aljanu yake.
Zance mafi inganci shi ne Shaiɗan aljani ne, saboda an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala'iku an halicce su ne daga haske, kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: (2996) yake nuni zuwa hakan, sannan Shaiɗan yana da zuriyya, wacce take hayayyafa, mala'iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga cikinsu yake ba, Wannan yasa za'a ɗauki ayar suratul Bakara a matsayin tana nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba, sannan mala'iku ba sa saɓawa Allah, shi kuma Iblisa yana saɓawa Allah.
Don neman Karin bayani duba: Tafsirin Ibnu-jarir 1/507 da Jami'u lada'if attafsir 1/278.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
SHAIƊAN YANA CIKIN JINSIN
ALJANU NE KO MALA'IKU?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikumus.
Da fatan Malam yana lafiya. shin Shaiɗan yana cikin jinsin aljanu ne Ko Mala'iku
kuma Dame Allah ya halacci mala'iku?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaykumussalam, to
ɗan'uwa malaman
tafsiri sun yi saɓani game da haka zuwa
maganganu guda biyu:
1. Shaiɗan yana daga cikin
mala'iku, saboda faɗin Allah a cikin
suratul Bakara aya ta 34:
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَىٰ وَاسْتَكْبَرَ وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Kuma a lokacin da
Muka ce ga mala'iku: ''Ku yi sujada ga Adam,'' Sai suka yi sujada, face Ibilĩsa
ya ƙi,
kuma ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kafirai.
Wannan ya nuna shaiɗan yana daga cikin mala'iku
ne.
2. Shaiɗan Aljani ne, saboda
faɗin Allah maɗaukakin sarki:
وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَائِكَةِ اسْجُدُوا لِآدَمَ فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ أَفَتَتَّخِذُونَهُ وَذُرِّيَّتَهُ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِي وَهُمْ لَكُمْ عَدُوٌّ بِئْسَ لِلظَّالِمِينَ بَدَلًا
Kuma a lokacin da
Muka ce wa malaiku, ''Ku yi sujada ga Adamu.'' Sai suka yi sujada face Iblĩsa,
ya kasance daga aljannu sai ya yi fasiƙanci ga barin umurnin
Ubangijinsa, To fa, ashe, kuna riƙon sa, shi da zũriyarsa,
su zama majiɓinta baicin Ni, alhali
kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzalumai.
(Suratul Kahf Aya ta 50).
Wannan ayar ta
bayyana cewa shaiɗan daga aljanu yake.
Zance mafi inganci
shi ne Shaiɗan aljani ne, saboda
an halicce shi ne daga wuta, su kuwa mala'iku an halicce su ne daga haske,
kamar yadda hadisin Muslim mai lamba ta: (2996) yake nuni zuwa hakan.
Sannan Shaiɗan yana da zuriyya,
wacce take hayayyafa, mala'iku kuma ba sa haihuwa, wannan sai ya nuna ba daga
cikinsu yake ba, Wannan ya sa za a ɗauki ayar suratul Bakara a matsayin tana
nufin yana daga cikinsu ta fuskar zaman tare, amma ba ta fuskar halitta ba,
sannan mala'iku ba sa saɓawa Allah, shi kuma
Iblisa yana saɓawa Allah.
Don neman Karin
bayani duba: Tafsirin Ibnu-jarir 1/507 da Jami'u lada'if attafsir 1/278.
Allah ne mafi sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu
Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.