𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, malam tambayata ita ce, wata ce saurayinta ya ba ta amana akan cewa
yana aiki, sai ya ce mata kar ta sake ta fada wa kowa yana da aikin yi ɗin, ita
kuma 'yan gidansu kullum sun nace mata saurayinta ba ya sana'a ba ya aikin
komai, ita kuma ba ta jin daɗi, sai kawai ta faɗi maganar yana aiki, gashi kuma
amana ya ba ta ita kuma gashi ta faɗa. To shin malam ta saɓa alkawari ne ko ta
ci amanarsa ne? Domin an ce babu kyau saɓa alkawari sannan kuma ta ci amanane
ko yaya ne saboda ta faɗa ne irin babu yadda za ta yi ne, ta gaji da zancen
mutane akan saurayinta ba ya Sana'a sai zaman banza.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam,
To ai baiwar
Allah ai ba zai yiwu ‘yan uwan su bar ta, ta aure shi alhali ba shi da sana'a
ba, ko kuma su aurar da ita ga wanda ba su san takamaiman sana'arsa ba, don
haka suka matsa domin susan sana'ar tasa, wannan shi ne kawai a tunanina.
Saboda Abuhurairata ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya ce: "Idan wanda kuka yarda
da addininsa da ɗabi'unsa ya nemi aure a wurinku, to ku aurar masa...". Tirmizhiy
1084, Ibn Majah 1967.
Yana daga
cikin ɗabi'un mutum kyawawa ya zama yana da sana'a, wannan na daga cikin abin
da zai sa a ba mutum aure, idan kuma mutum ba shi da sana'a, hakan shi ma zai
iya sa a hana shi aure. Saboda haka nake ganin wannan ba za a sa shi a cikin
cin amana ko saɓa alƙawari ba, saboda ai dama dole ne sai an san sana'arsa
kafin a ba shi aurenta idan za a bi ƙa'ida, saboda kada a ba mai zaman kashe
wando mata ta yi ta rayuwa cikin ƙunci ta dalilin lalacin miji.
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.