𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum, malam mahaifiyata tana fushi da ni saboda na ki mayar da 'ya'yana
kanana gurin ubansu, kuma abinda ya sa na rabu da shi ba shi da aikin yi sai
shaye shaye da bin mata, kuma har yanzu ba shi da aure a tasha yake kwana,
saboda gidan hayar sun kore shi, kuma mahaifansa sun rasu, amma na fahimtar da
ita makota sun fahimtar da ita amma ta ki, a yanzu haka sai makota ne suka ba
ni wurin zama nake Sana'a nake kula da karatun 'ya'ya nawa, shin Allah zai kama
ni da fushin nan nata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salamu, A shar'ance, wadda ta fi cancanta da kuma haƙƙin kula da ƙananan 'ya'ya
ita ce mahaifiyarsu har sai ta yi aure, ko da kuwa mahaifin nasu ba shi da
matsalar kulawa da su, sai dai fa idan mahaifiyar tana da kasawar kula da su,
ko kuma ta sarayar da haƙƙin ga shi mahaifin yaran, saboda hadisi ya tabbata
daga Abdullahi ɗan Amru cewa; Lallai wata mata ta ce:
"Ya
Manzon Allah, lallai wannan ɗan nawa ya kasance cikina shi ne jaka ta rayuwa a
gare shi, cinyata ita ce shimfiɗarsa, nonona kuma nan ne abin shansa, sai ga
shi mahaifinsa yana yunƙurin kwace shi daga gare ni" sai Annabi ﷺ ya ce
mata: "Ke ce kika fi cancanta da riƙe yaron matuƙar ba ki yi aure
ba"".
Duba
Musnadul Imami Ahmad 6707, ko Abu Dáwud 2276, ko Sunanud Dáraƙuɗniy 3808.
Wannan
hadisi dalili ne da ke nuna cewa a matsayinki na uwa, ke ce kike da haƙƙin kula
da tarbiyyar waɗannan ‘ya’ya, kuma haƙƙi ne na wajibi a kan iyaye su ba ‘ya’yansu
kyakkyawar tarbiyya, babu wani mahaluƙi a bayan ƙasa da ya cancanta ya hana
iyaye su ba ‘ya’yansu kyakkyawar tarbiyya matuƙar ana aiki da abin da ya
kamata, daƙile wannan damar a tsakanin ‘ya’ya da iyayensu, ba abu ne mai kyau
ba. Kuma ba a yin biyayya sai ga abin da yake dai-dai ne a Shari'a, shi kuma
wannan umurni na mahaifiyar taki ba za a lissafa shi a cikin abin da yake
dai-dai da Shari'a ba, saboda matuƙar aka mayar da ‘ya’yan nan ga irin wancan
uban, to tarbiyyar ‘ya’yan nan zai shiga mummunan hali, sai hakan ya sa ba za a
lissafa ki a cikin waɗanda suka ƙuntata wa iyayensu ba saboda wannan umurni na
mahaifiyarki ya saɓa wa Shari'a, dalili a kan haka shi ne:
Ya tabbata a
hadisin Manzon Allah ﷺ cewa: Lallai Annabi ﷺ ya aiki wata runduna, sai ya sanya
wani mutum ya shugabance su, sai wannan mutumin ya kunna wuta, ya ce wa waɗannan
Sahabban su shiga wannan wuta, sai wasu suka yi nufin shiga, sai sauran mutanen
suka ce: to ai wutar muka guje wa (ta yaya kuma za mu shige ta?), da suka dawo
sai suka ba Manzon Allah ﷺ labari, sai Manzon Allah ﷺ ya ce ma waɗannan da suka
yi nufin shiga wutar: "In da kun shiga cikinta, da ba za ku gushe ba kuna
cikinta har zuwa ranar Alƙiyama", sai ya faɗi magana mai kyau ga waɗanda
ba su yi nufin shiga ba ya ce: "Babu biyayya ga saɓa wa Allah, biyayya ana
yin ta ne ga abin da yake dai-dai".
Bukhariy
7257, Muslim 1840.
Wannan
hadisin yana nuni a kan cewa ba a yi wa kowa biyayya sai a abin da yake ya dace
da shari'a, saboda idan da a ce biyayya ana yin ta ba tare da lura da kyau ko
rashin kyau na abin da za a yi biyayya a kai ba, to da Manzon Allah ﷺ ya goyi
bayan wancan mutumin da ya shugabantar a kan shiga wutar da ya ce mabiyansa su
yi. Wannan sai ya zama dalili da ke nuna cewa ƙin bin umurmin mahaifiyarki
wajen mayar da waɗannan ‘ya’ya naki ga mahifinsu da shi kan shi ba shi da
tarbiyyar kulawa da su bai zama laifi ba, ballantana Allah ya kama ki da laifin
uƙuƙul walidain (wato ƙuntata wa iyaye).
Allah ne
mafi sani.
Jamilu
Ibrahim Sarki, Zaria.✍🏻
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.