MAFITAR MATA 01 Mafi Yawan '‘Yan Wuta Mata Ne

    Babu shakka mata da yawa suna mamaki akan wane daliline ya sa akace sune mafi yawa a cikin wuta.

     Abdullah Ɗan Umar (R.A) Ya ce:

     Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

    Na tsinkayi Aljanna, sai naga mafi yawan ahalinta talaƙawa ne, kuma na tsinkayi wuta, sai naga mafi yawan ahalinta mawadata ne da mata.

    [Ahmad ne ya rawaito shi]

     Abu Huraira (R.A) Ya ce:

     Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

    Na tsinkayi wuta sai naga mafi yawan ‘yan cikinta mata ne, kuma na tsinkayi Aljanna sai naga mafi yawan ‘yan cikinta talaƙawa ne.

    [Ahmad ya rawaito shi].

    Sannan a wani hadisin Matan Imran ɗan Husain sukace: Ya bamu labari cewa:

     Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

    Mafi ƙarancin mazauna Aljanna mata ne.

    Waɗannan hadisai suna nuni da yadda mata da kuma masu tarin dukiya za su iya samun kansu a ranar Alƙiyama matuƙar basu kiyaye dokokin ALLAH ba.

    Mene ne Dalili?°

    Dalilan suna da yawa amma za mu kawosu ɗaya bayan ɗaya tare da bayanansu, kuma muna fatan '‘yan uwa mata za su kiyayesu.

    1• Shirka

    Shirka ita ce mafi girman zunubin da ALLAH baya yafewa har sai mai yinta ya nemi a yafe masa kafin ya koma ga ALLAH, amma mutuƙar ya koma ga ALLAH bai tuba ba, to zai shiga wuta ya kuma dawwama a cikinta.

    Kamar yadda ALLAH ya faɗa a cikin sura Al-Nisa Ayata 48-116.

     Idan akace shirka wato ita ce bautar wanin ALLAH, kamar jiɓinta lamari gareshi ga wani wanda ba ALLAH ba, wato mace taje gurin boka ta miƙa masa dukkan damuwarta, da nufin shi ne zai magance mata matsalarta,

     Kamar neman waraka daga wata cuta, ko neman mallake miji, ko cutar da abokiyar zaman aure (kishiya) ko abokiyar kasuwanci ko neman wani abin duniya dai.

     Wannan kai kukan gurin boka, shi ne haɗa ALLAH da wani, duk da dai shirka kashi-kashi ce, shi kuma boka yana bin umarnin aljanu ne, su kuma aljanu basa biyan buƙata dole sai sunsa mutum ya kafircewa ALLAH, kota hanyar sawa a yanka wata dabba, ko susa mace ta rinƙa lesbian, ko susa bokan ya yi zina da ita, ko ya bata wani abu yace taje ta binne na shirka, ko a sata ta yi tsarki da wani abu ko tasa wani nama agabanta ya yi kwanaki sai ta dafawa mijinta yaci dadai sauransu.

     Dukkan waɗannan abubuwa yinsu bin umarnin shaiɗan ne, kuma yana kaiwa ga shirka, hakan kuwa yana sawa mace ta shiga wutar ALLAH.

    2• Sihiri

    Sihiri yana ɗaya daga cikin abinda yake shigar da mutum wuta, wanda kuma mata da yawa suna bashi mahimmanci sosai.

     Shi sihiri kafirci ne, kamar yadda ALLAH ya faɗa a cikin Alkur'aninsa cewa:

     Sai dai su shaiɗanu ne suka kafirta suna koyawa mutane sihiri, Baƙarah Ayata 102.

     Kenan shi sihiri yinsa kafirci ne, kuma mai yinsa da wanda ya sa a yi masa sun kafirta.

     Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

    Wanda yaje wajen duba, ya gasgata akan abinda yake faɗa, toya kafirwa abinda aka saukarwa Annabi {s.a.w}.

    [Abu Dawud, Tirmizi da Ibn Majah].

     Wato ya kafircewa Alƙur'ani da sunnah, wanda kuwa ya kafirce musu, ya zama kafiri ɗan wuta, kuma zai dawwama a cikinta har sai ya tuba kafin mutuwa ta zo masa.

     Manzon ALLAH {s.a.w} Ya ce:

    Wanda yaje wajen ɗan duba bai gasgata abinda yake faɗa masa ba, to baza a karɓi sallarsa ba ta kwana arba'in (40).

    [Ahmad da Tirmizi da Nisa'i].

     Don haka dukkan waɗannan ayyukan suna kai mata i zuwa jahannama, kuma wasu kullum ƙara zurfi sukeyi a cikinsa, duk da cewa akwai maza ma masu zuwa gurin bokaye da masu duba.

     Ita duba ita ce mutum yaje a duba masa mezai faru akan kasuwancinsa, ko akan mijin da zata aura ko matar da zaka aura, wai akwai alkhairi ko babu, idan anyi auren.

     Hadda masu cewa ai burujinku baizo ɗaya ba, idan ka aureta wahala zakasha, kai kace wahayi ake musu, dukkan masu wannan da'awar ƙarya sukeyi, abinda suke aikatawa kafirci ne.

     Babu wanda ya isa yasan abinda zai faru da wani sai ALLAH shi kaɗai ya barwa kansa sani, ko Annabawa basa sanin komai sai iya abinda ALLAH ya sanar dasu ta hanyar wahayi.

    ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

    ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

    Mu haɗu a darasi na gaba.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.